Yanzu-Yanzu: Singapore ta jingine shirye-shiryen Aikin Hajji zuwa 2021

0
7

Babbar Majalisar Addidinai ta Singapore, wacce a kewa lakabi da (MUIS), ta bayyana cewa za ta jingine shirye-shiryen Aikin Hajjin 2020 ga Alhazan ta 900 sai zuwa 2021 sabo da annobar COVID-19. 
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, 15 ga Mayu, MUIS ta ce ta cimma matsayar ne bayan ta tuntubi Hikumar Lafiya ta kasar. 
“Kwamitin Fatawa ya kira taron tattaunawa a kan batun ya kuma goyi bayan matakin jingine shirye-shiryen Aikin Hajjin zuwa badi domin kare lafiyar mahajjanatan kasar,” in ji MUIS. 
Kwamitin na da ra’ayin cewa a halin da a ke ciki, ba kowanne sharaddai na kafin Aikin Hajji Singapore ta cika ba, saboda haka sun yanke cewa kawai a jingine batun hajji domin gujewa matsaloli. 
Maniyyatan 900, wadanda suke tsarin Hajjin bana, sune dai za su je Aikin Hajjin 2021 din

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here