Da DUMI-DUMI: Saudiyya za ta sassauta dokar kulle, a ci gaba da harkoki, komai ya dawo daidai

0
319


Daga Mustapha Adamu
A yau, Talata ne, Saudi Arebiya ta sanar da sassauta duk wata dokar kulle da ta kakaba sakamakon annobar coronavirus, in da za a dawo harkokin cinikayya, kafin daga bisani ta sanya ranar da za a bude kasar gaba daya domin komai ya dawo daidai kamar da. 
Jaridar Al Arabiya English ta rawito cewa daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Mayu, Saudiya za ta saki gari a rika fita daga karfe 6 na safe zuwa karfe 3 na yamma a duk fadin kasar, amma banda birnin Makkah. 
Za a ci gaba da shige da fice tsakanin jihohi da birane har zuwa awannin da a ka sanya na hana zirga-zirga. 
Za kuma a bude harkar cinikayya a manya da kananan kantuna na kasar. Amma kuma za a ci gaba da rufe duk wasu harkoki da a ka san cewa zai yi wuya a samu bada tazara da juna, kamar a shagunan kwalliya na mata, shagunan aski, guraren wasanni, guraren shakatawa, guraren motsa jiki da dakunan kallon fina-finai. 
Hakazalika, daga 30 ga watan na Mayu zuwa 20 ga watan Yuni, Saudiya za ta bari a ci gaba da zirga-zirga a ko ina a kasar daga karfe 6 na safe zuwa karfe 8 na yamma, amma banda birnin Makkah. 
Za a dage dakatar da ayyuka, inda ma’aikata na ma’aikatun gwamnati da ma’aikatu ma su zaman kan su za su koma aiki, su kuma ci gaba da aiki a ofisoshin su kamar yadda a ka saba, amma fa sai sun bi sharuddan kariya da ma’aikatar lafiya ta gindaya. 
Haka kuma za a dage dakatarwar zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida, amma shima sai an yi riko sosai da matakan kariya da mahukuntan ma’aikatar sufurin jiragen sama  da kuma hukumar lafiya ta kasar su ka gindaya. 
Za a bude guraren saida abinci da kayan sha, kamar su lemo da shayi, tare da karfafa dokar bada tazara da juna a duk guraren da jama’a suke harkoki a ko da yaushe. 
Za kuma a ci gaba da hana tarukan jama’a da su ka haura mutum hamsin, kamar taron bikin aure ko jana’iza. 
Daga ranar 21 ga watan Yuni kuwa, komai zai dawo daidai a ko ina a fadin Saudiya,  amma banda birnin Makkah, in da kasar ke fatan dawowa kamar da, kafin lokacin a saka dokar kulle. 
Haka kuma IHRHausa ta jiyo cewa Saudiya za ta bude masallatai a daukacin kasar domin bawa al’umma damar ci gaba da sallolin jam’i a masallatai, amma shima sai an yi riko da matakan kariya da ma’aikatar lafiyar kasar ta gindaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here