Rahotanni daga Saudi Arebiya sun bayyana cewa a ranar 31 GA watan Mayu za a bude Masallacin Harami na Madina domin al’umma su ci gaba da ibada a ciki.
IHRHausa ta rawaito cewa wannan ci gaban ya zo ne sakamakon sassauta dokokin hana zirga-zirga da za a yi nan ba da dadewa ba a Saudiya.
Rahoton ya nuna cewa, “bayan da za a dage dokar hana zirga-zirga a kasar, mutane daga ko wanne garuruwa za su iya zuwa ziyara Masallacin.”
Amma kuma rahoton ya jaddada cewa har yanzu dokar hana zuwa ziyarar daga wasu kasashen tana nan daram, har sai yadda ta yiwu.