COVID-19: Sama da masallatai 90,000 za a sake budewa a Saudiya

0
368

A ranar Lahadi ne za a bude masallatai 90,000 a fadin Saudi Arebiya bayan da a ka rufe su a sama da watanni biyu da su ka gabata sakamakon annobar cutar COVID-19, wacce a ka fi sani da coronavirus. 
Tuni ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci da ma’aikatan ta su ka fara gyare-gyare, goge-goge da tsaftace masallatan, manya da kanana a fadin kasar, amma banda birnin Makkah. 
Jaridar turanci mai fitowa killum, Khaleej Times, wacce a ke wallafa ta a Dubai ta bayyana cewa za a bude masallatan ne a kan gwadaben sharuddan da Ministan Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci Dakta Abdullatif Al Asheikh, da kuma shawarwarin da manyan jami’an kwamitin malamai ta bayar. 
Haka kuma Ma’aikatar ta fara wani gagarumin kamfe ta kafafen yada labarai domin fadakar da masallata a kan matakan kariya domin dakile yaduwar COVID-19. 
Matakan kariyar sun hada da yin alwala a gida, goge hannu da sinadarin tsaftace hannu da kuma wanke hannun kafin tafiya zuwa masallaci da kuma bayan an dawo gida. 
An kuma shawarci tsofaffi da masu cututtukan da su ka yi tsanani da su zauna a gida. An kuma bada shawarar karanta Kur’ani ta yanar gizo-gizo daga wayar hannu ko kuma ta littafin amma mallakar mutum shi kadai ba na jama’a ba. 
Haka zalika an umarci masallata da su rika tahowa da dardumar sallar su daga gida, sannan su rika yin sahu ta hanyar yin nesa da juna na a kalla mita biyu a yayin kowacce sallah. 
Haka kuma an hana yara ya’n kasa da shekara 15 zuwa masallatan. 
Dole sai kowa ya sa takunkumi, sannan an hana gaisawa da hannu da sauran nau’in gaisuwa bayan an idar da sallah. 
Haka kuma Ma’aikatar ta kuduri aniyar tsaftace da kuma gyare-gyaren masallatan a fadin masarautar Saudiya,  kuma za a yi aikin ne daidai da yadda hukumomin lafiya na duniya su ka amince. 
Wannan ya hada da wayar da kan masallata a sama da masallatai miliyan 10 a fadin duniya, da kur’ainai sa da miliyan 43, sama da kantoci na ajiye Kur’ani 600,000, gami da gyara da alkinta wajen alkinta ruwa sama da 176,000 da ake ajiyewa a masallac

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here