Daga ranar Lahadi, dukkanin bankuna da ma’aikatun hada-hadar kudade za su dawo cikakken aiki, in ji wata ma’aikatar hada-hadar kudade ta Saudi Arebiya (SAMA).
Babban bankin masarautar ya kara da cewa dukkanin harkokin sana’o’i za su dawo a hankali, yayin da kuma za a rika yin ayyuka ta la’akari da matakan kariya domin a tabbatar da cewa ma’iakata sun dawo ofisoshin su kuma suna aiki lafiya lau.
Dawowar ma’aikatan na gudana ne daki-daki daidai da tsarin kowanne banki. Wannan ya hada gudanar da ayyuka cikakku a rassan ko wanne banki da kuma ciniyoyin sa na aika kudade, kuma a awannin da a ka saba yin aiki, kamar yadda SAMA ta bada umarni kafin a kulle kasar.
A wata sanarwa da ta aikewa Okaz/Saudi Gazette, SAMA ta ce “matakin dawowar na kunshe a cikin umarnin da masarauta ta bayar ranar 26 ga Mayu ga ma’aikatan gwamnati, ma’aikatan hukumomin gwamnati, ma’aikatu masu zaman kan su da su dawo ofisoshin su kamar yadda Hukumar Kula da Ma’aikata da ci gaban Al’umma ta yi umarta,”
Haka zalika Ma’aikatar Lafiya da sauran hukumomin da abin ya shafa ne su ke tsara yadda dawowar ma’aikatan za ta kasance.
Daga 21 ga Yuni, duk lardina da biranen Masarautar za su dawo yin rayuwa kamar da kuma daidai da sharuddan da a ka saba gindayawa kafin a saka dokar kulle, sai dai ban da garin Makkah. Sannan kuma dole sai an bi dokoki da matakan kariya da kuma yin nesa da juna kamar yadda hukumomin lafiya su ka umarta.