Sababbin bayanai kan bude Masallacin Madina

0
560

Yayin da Saudi Arebiya ta sanar da bude Masallacin Harami na Madina ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, Ma’aikatar Kula da Masallatan Harami Biyu Ma su Tsarki sun bayyana tsare-tsaren yadda za a rika yin sallah a Masallacin. 
Daga tsare-tsaren, an bawa masallata maza su rika shiga masallacin ta Alhijra kofa ta 4, Quba, kofa ta 5, King Saud, kofa ta 8, Imam Al-Bukhari, kofa ta 10, King Fahd, kofa ta 21, King Abdul’aziz, kofa ta 34 da kuma Makkah, kofa ta 37, in da kofar Salam za ta ci gaba da zama a rufe. 
Sannan kuma iya harabar masallacin na Madina kawai a ka yarda masallata su shiga, da kuma bangaren fadada masallacin mai suna King Fahd. 
An dakatar da ziyara zuwa tsohon masallacin Ma’aiki da kuma Rawdah, in da kabarin Annabi Mai Tsira da Amincin Allah ya ke. 
Sannan kuma da zarar kashi 40 na masallata sun shiga masallacin to za a rufe shi domin hana cunkoso. 
An kuma cire dukkanin shimfidar da ke masallacin, inda masallata za su rika yin sallah a tantagaryar kasa. 
A karshe kuma, an dakatar da bude baki na azumi a masallacin a halin yanzu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here