SAUDI AREBIYA: Yawan mutanen da su ka warke sun fi wadan da su ka kamu da COVID-19

0
303

Daga Mustapha Adamu
Hukumar Lafiya ta Kasar Saudi Arebiya ta bayyana cewa mutanen da su ka warke daga cutar COVID-19 sun fi wadan da su ka kamu da cutar yawa a fadin kasar. 
Saudi Press Agency (SPA) ta fadi ta bakin Kakakin Hukumar Lafiyar, Dr Muhammad Al-Abdel an samu karin mutum, 1,618 da su ka kamu da cutar a cikin awa 24, in da adadin masu dauke da cutar a kasar ya kai 83,384.
Amma duk da wannan gagarumin karin da a ka samu, adadin wadan da su ka warke daga cutar ya fi yawa, bayan da karin mutum 1,870 su ka warke, inda adadin wadan da su ka warke a halin yanzu ya kai 58,883.
Hukumar ta kara da cewa bayan da wasu karin mutum 22 da ke dauke da cutar su ka rasa rayukan su, adadin wadan da cutar ta kashe a kasar ya zama 480 kenan, kuma ba wani gagarumin adadi bane, in ji Dr  Al-Abdel. 
Jihar Riyadh ce ke ci gaba da jan ragama a jerin garuruwan da a ka samu bullar cutar da 679, sai Jeddah da ke biye mata da 247, 105 a Makkah, 101 a Hufof, 84 a Dammam, 64 a Al-khobar, 45 a Madina, 33 a Buraidah, 25 a Qatif, 24 a Dhahran. An samu sababbin wadan da su ka kamu a burnin Al-Madha, 13 a Taif, Tanura da Tabuk na da 12 kowacce, sai Bulhria da ke da 10.
Sauran masu dauke da cutar sun watsu a wasu kanan birane da kuma gundumomi a fadin masarautar, in ji Dr Al-Abdel. 
Cutar ta kama mutum 5,945,737 a fadin duniya inda ta kashe mutum 365,368 sannan mutane 2,507,354 sun warke

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here