DA DUMI-DUMI: Indonesia ta fasa zuwa Aikin Hajjin bana

0
198

Daga Mustapha Adamu
Ma’aikatar Harkokin Addini ta Indonesia ta yanke shawarar fasa zuwa Aikin Hajjin 2020 sakamakon matsalar annobar cutar COVID-19 da ta addabi Saudi Arebiya, wacce ta yanke hukuncin rufe hanyoyin ta saboda masu shigowa daga kasashen waje. 
Ministan Harkokin Addini na kasar, Fachrul Razi ya yi bayanin cewa cutar wacce ta addabi duniya ta kawo nakasu wajen cakuduwar al’umma a guraren yin ibada, shi ya sa tun farko Ma’aikatar ta kirkiro da cibiyar lura da matsaloli na Hajjin 2020.
“Cibiyar ta yi wani nazari har kala uku a wasu fannoni a kan Hajjin 2020” in ji Fachrul a ganawar da ya yi da manema labarai a yau. 
Bayan nazarin, cibiyar ta fitar da zabuka uku da su ka maida hankali a kan kasar ta je Aikin Hajjin yadda a ka saba, ko ta rage yawan maniyyata ko ma ta fasa zuwa kwata-kwata, amma daga karshe sai gwamnati ta zabi a fasa zuwa kwata-kwata. 
Ministan ya tuna cewa gwamnatin kasar ta taba soke zuwa Aikin Hajjin lokacin da sojojin kasar Holland su ka yi mata kama karya. 
Fachrul ya kara da cewa har yanzu ita ma Saudiyan ba ta bawa ko wacce kasa a fadin duniya tabbacin zuwa Hajjin ba.
“Kaga kuwa gwamnatin mu na da kankanin lokaci, ko ma ba lokacin da za ta yi shirin Aikin Hajjin,” in ji Ministan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here