Tsohon Shugaban Kungiyar Kamfanonin Jigilar Hajji da Umarah masu zaman kan su, AHUON, kuma Shugaban Visa Travels and Tour Ltd. ya yi kira ga Kamfanonin da su bullo da wasu hanyoyi na hadin gwiwa in dai su na son su tsallake matsalar tattalin arziki da ta addabi harkar sufurin sama.
Tsohon Shugaban, wanda ya yi jawabi a taron wayar da kai da AHUON din ta aiwatar, ya kuma yi kira ga masu harkar da su hada kan su su nemi tallafi daga wasu hukumomi kamar su NCAA domin bawa masu harkar sufuri masu zaman kan su tallafi domin su rage radadin asarar da su ka tafka sakamakon dakatar da Umarah da sabo da annobar Coronavirus.
AHUON ce ta shirya taron mai taken “Makomar jigilar Aikin Hajji da Umarah bayan annobar Coronavirus” wacce kungiyar ta hada a karkashin jagorancin Salisu Butu.
HAJJ REPORTERS ma na cikin kungiyoyin da su ka hakarci taron da a ka yi ta yanar gizo na tsawon awanni biyu.
Tun da farko, Jagoran masu jawabai a taron, Yinka Folami, Shugaban Travels and Logistics Centre ya yi irin wannan kiran sabo da a kan abin da ya suffanta da halin tantalbatete da harkar jigilar Hajji da Umarah ta shiga.
Yinka Folami ya kara da cewa akwai bukatar ya’n kungiyoyin da su kwantar da hankalin su game da irin rashin tabbas din da COVID-19 ta kawo. Ya kuma yi kira da a yi riko da kwarewa a harkar da kuma yin aiki tukuru domin hakan shine maganin fita daga wannan mawuyacin halin da a ke ciki.
A nashi bangaren, Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Kasa (NAHCON), Alh. Zikrullah Kunle Hassan, wanda na daya daga cikin manyan masu jawabi, ya tabbatarwa AHUON cewa, “NAHCON ba za ta bari takwarar ta ta durkushe ba sabo da wanzuwar su, wanzuwar NAHCON ce,”
Zikrullah ya kuma bayyana cewa mai yuwa Saudi Arebiya ta hana tsofaffi da kuma mutanen da su ke fama da wasu cututtuka zuwa Hajjin 2020 idan har daga karshe ta yanke shawarar Aikin Hajjin na bana.