TA NA KASA TA NA DABO: Malaysia za ta yanke hukincin zuwa Hajjin 2020 a makon gobe

0
176


Daga Mustapha Adamu
Minista a bangaren ofishin Fira Ministan Malaysia, Zulkifili Mohamad Al-Bakri a makon gobe ne za a sanar da ko musulman kasar za su je Aikin Hajjin bana ko na za su je ba. 
Zulkifili, wanda shi ne shugaban sashen  harkokin addinai ya ce an riga an tattauna da Asusun Hajji na kasar mai suna Tabung Haji. 
“Za a gabatar da sakamakon tattaunawar a gaban majalisar zartaswa kafin a sanar da matakin ga ya’n kasa,” in ji shi, a wata sanarwa da ya fitar a yau. 
Tun a baya, Babban Mimistan Tsaro, Ismail Sabri Yaakob ya ce ba za a bayyana wata matsaya a kan ko musulmai za su je Aikin Hajjin bana ba sai an ji matakin da Saudi Arebiya ta dauka. 
“Da zarar Saudi Arebiya ta sanar da matsayar ta, to Mimistan Harkokin Addinai zai bayyana ta mu matsayar,” in ji Ismail

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here