YANZU-YANZU: Saudiya ta kuma sanya dokar kulle a Jiddah

0
193

Mahukunta a kasar Saudi Arebiya sun kara daukar wasu kwararan matakai na kariyar lafiya a birnin Jiddah na tsawon kwana 15, zai fara daga ranar Asabar, 6 ga watan Yuni zuwa 20 ga Yuni, kamar yadda jaridar Saudi Press Agency ta fadi ta bakin wata majiya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida

Wasu manyan mahukunta ne su ka dauki wannan matakin bayan yin nazari a yanayin yaduwar cututtuka da kuma cunkoso a dakunan kula da cututtukan da su ka ta’azzara a birnin. 
Matakan kullen da a ka sake kakabawa birnin na Jiddah sun hada da: 
– An sake sanya dokar hana zirga-zirga a birnin daga karfe 3 na yamma zuwa karfe 6 na safe. 
-An sake dakatar da yin sallah a masallatai. 
-An sake dakatar da zuwa ma’aikatu na gwamnati da masu zaman kan su da kuma kamfanoni masu zaman kan su. 
-An sake rufe guraren cin abinci da shaye-shaye. 
-An hana taron mutane da ya wuce mutum 5.
Amma kuma za a ci gaba da harkokin sufuri na sama da kasa a ciki da wajen burnin ko da a cikin kokacin dokar hana zirga-zirgar ne

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here