Da wuya Aikin Hajjin 2020 ya yiwu”: Za a fara maidawa maniyyata kudaden su a India

0
227



Duk maniyyatan da su ke son su fasa Aikin Hajjin bana sakamakon annobar cutar coronavirus da ta mamaye duniya, to za a maida musu da kudaden su daidai adadin da su ka biya, in ji Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin Hajji na India, Masood Ahmed Khan, ranar Asabar. 
Kwamitin Kula da Harkokin Hajji an kafa shine bisa doka daga majaliasar kasa kuma yana karkashin Hukumar Kula da Al’umma marasa Rinjaye ta kasar India. 
Khan ya ce makonni kadan ne su ka rage a fara shirye-shiryen Aikin Hajjin amma har yanzu babu wata sanarwa daga Mahukuntan Saudi Arebiya a kan za a yi Aikin Hajjin ko ba za a yi ba. 
“Zai yi wuya a yi Aikin Hajjin bana. Har wadan da ba su rubuto bubatar su ta karbar kudaden su ba, su ma za a basu gaba daya kudaden su,” Khan ya fadawa PTI. 
Adadin musulmai 20,000 ne za su ka yi niyyar zuwa Aikin Hajjin bana daga India

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here