Yawancin maniyyata a Thailand sun fidda ran Aikin Hajjin bana sai zuwa badi

0
185

Maniyyata 5,700 ne a Thailand suke shirin fasa tafiya Aikin Hajjin bana sakamakon annobar cutar coronavirus, in da za su bari sai badi idan Allah Ya kai mu sai su je.

Kamar yadda Cibiyar Raya Al’adu ta Kasar Iran a Bangkok ta bayyana, maniyyata 8,000 ne daga Thailand su ka yi rijistar zuwa Hajjin bana.

Amma kuma wadan da su ke da niyyar zuwa Saudi Arebiya idan za a yi Aikin Hajjin bana, to dole su yi riko da sharuddan lafiya da a ka gindaya domin kariya daga kamuwa da cutar.

Har yanzu dai Hajjin 2020 na fuskantar rashin tabbas sabo da annobar coronavirus.

A tuna cewa, a watan Afrilu, Saudiya ta dakatar da Umara da a ka saba yi a tsawon shekara sabo da fargabar coronavirus da ta yadu a fadin kasar.

Kawo yanzu dai Saudiya ba ta fadi matsayar ta cewa za a yi Aikin Hajjin bana da a ka sanya za a yi a karshen watan Yuli ko ba za a yi ba.

A watan Mayu, Saudiya ta bawa kasashen muslmai shawara da su dakatar da shirye-shiryen Aikin Hajjin na bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here