Hajjin 2020: Da yiwuwar a mayar wa da maniyyata kudaden su a South Africa

0
255

Hukumar Lura da Hajji da Umrah ta South Africa (SAHUC) ta bayyana cewa za ta gana da Bangaren kula da Harkokin Ƙasashen waje domin tattaunawa a kan Hajjin bana, wan da a ke sa ran za a yi nan da makonni kaɗan ma su zuwa. 
SAHUC ta bayyana cewa a ko da yaushe ta na tattaunawa da Hukumar Kula da Aikin Hajji da Umrah ta Ƙasar Saudi Arebiya da kuma ofishin jakadancin Saudiyan a South Africa, amma har yanzu ba ta samu wani jawabi kan za a yi Hajjin bana ko ba za a yi ba.
A watan Afrilu, Ministan Kula da Hajji na Saudi Arebiya, Dr Muhammad Saleh Benten ya yi kira ga Ƙasashen musulmi da su dakata har sai an ga yanayin coronavirus kafin a tabbatar da za a yi Aikin Hajjin bana. 
Yayin da lokacin Aikin Hajjin ke ƙaratowa, a na jira a ji matakin da Hukumar Hajji da Umara za ta dauka a kan za a yi ko ba za a yi ba saboda annobar COVID-19. 
Shi kuma Shugaban SAHUC, Shehen Essop ya bayyana cewa su na jiran su ji daga bakin Saudiya a kan matsayin Hajjin na bana. 
Essop ya ƙara da cewa ko da Saudiya ta dauki matakin yin Hajjin, to Alhazzan South Africa ba za su ta shi ba har sai ƙasar ta su ta bude iyakokin ta.
“Ba na jin mahajjatan za su samu wannan kulawar ta musamman a wannan lokacin,”
Ya ƙarar da cewa, yayin da kamfanonin jigilar alhazai su ka nuna aniyar su ta maidowa da maniyyata kudaden sh idan Saudiyya ta fasa yin Aikin Hajjin bana, har yanzu ba a samu bayanin dawo da kudade ba daga kamfanonin sufurin jirgin sama.
Essop ya ƙara da cewa duk maniyyatan da su ke da sha’war fasa Aikin Hajjin na bana za su iya tuntubar SAHUC domin karbar kudaden su, kuma duk abin da su ka kashe wajen yin rijista shima za a dawo musu da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here