YANZU-YANZU: Tsohon Shugaban NAHCON, Mukhtar ya yi magana kan Hajjin 2020

0
226

Tsohon Shugaban Hukumar Kula Da Hajji ta Kasa, NAHCON da ya sauka kwanan nan, Barista Abdullahi Muhammad Mukhtar ya ce “neman soke Aikin Hajjin bana da a ke yi abin bakin ciki ne ga hukumar da ba za ta samu damar sauke nauyin ta ga maniyyata ba,  su ma kuma ba za su samu damar sauke farali ba.”

Barista Mukhtar na ɗaya daga cikin ƙwararru a harkar Hajji da Umara a duniya da su ka zo da wasu dabaru na yadda Saudi Arebiya za ta shirya Hajjin bana.

Tsohon Shugaban ya faɗawa Taron Ma su ruwa da Tsaki a kan harkokin Hajji da Umrah (WHUC) hakan ne lokacin da a ka nemi jin shawarwari daga ƙwararru a harkar a kan yadda za a gano bakin zaren a samu a yi Aikin Hajjin bana, kamar yadda ya ke ƙunshe a wata sanarwa da a ka aikowa INDEPENDENT HAJJ REPORTERS ranar Alhamis.

Sanarwar ta faɗo ta bakin Mukhtar da cewa “Ƙin yin Aikin Hajjin bana abin bakin ciki ne ga harkokin kasuwanci da za su tafka manyan asarori. Haka zalika hukumomin Aikin Hajji  ba za su samu damar sauke nauyin su ga maniyyata ba,  su ma kuma ba za su samu damar sauke farali ba.”

Ya yi bayani cewa “ɗaya bangaren wannan bakin cikin shine dubun dubatar mutanen Saudiya da su ka saba da tarbar baƙi. Mutane ne da su ka tashi su ka ga ana yin Aikin Hajji sama da shekaru 1400. Wata al’umma ce da za ta ga a karo na farko a zamanin nan ba a yi Hajji ba sakamakon wata cuta da ta bullo a wata ƙasar amma a ke yaki da ita a kasa mai tsarki. Har ta kai ga ana bawa musulmai a faɗin duniya haƙuri cewa su ƙara haƙuri, ana iya bakin ƙoƙari. Ba a son a sarayar da rayuwar wasu ne. A dai ci gaba da addu’a kamar yadda muma mu ke yi.”

“COVID-19 ta sanya sai dai mu riƙa zama nesa da juna. Idan mutum biyu su ka haɗu, hakan ka iya zama haɗari a gare su. Mun dena yin musabiha da hannu ko da runguma. Sai dai mu tsaya tsawon mita 2 da juna. Mu riƙa tambayar wannan mutumin wanene shi, daga ina ya ke?”

Mukhtar ya kuma yabawa Ƙasa mai tsarkin a bisa jajircewar ta wajen tsare-tsare kamar yadda ta saba a shekarun baya. Ya ce “manyan matakai a na daukar su ne ido da ido. Dubban ganawa ma su amfani da a ka saba yi kafin a fara Hajjin sun dawo sai dai ta yanar gizo kuma hakan ya sanya Aikin ya samu tasgaro.”

Ƙasar Saudiya wacce take abar alfahari, mai ɗauke da birane biyu mafi tsarki wato Makkah da Madina, ga Ka’aba, ta kasance abar ƙauna ga miliyoyin alhazai a faɗin duniya. Inda ƙasar ke tarbar su ba ma a matsayin mai karbar baƙi ba, a matsayin wacce ta yi imani da sunnonin Ma’aiki, Annabi Muhammad Dan Abdallah, Tsira da Amincin Allah su Kara Tabbata a Gare shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here