Shin kun san dalilin da ya sanya Malaysia ta fasa zuwa Hajji?

0
254

A ranar Alhamis ne Malaysia ta yanke hukuncin fasa tura ƴan ƙasar zuwa Aikin Hajjin 2020.
Annobr COVID-19 ce dalilin da ya sanya ƙasar ta dauki wannan mataki.
Ministan Kula da Harokin Addinai, Zulkifli Mihamad Al-Bakri ne ya sanar da matakin a yayin ganawa da  manema labarai a Putrajaya.
Malaysia na da mutane 8,639, da su ka haɗa da mutum 7, 014 da su ka warke sannan mutane 188 su ka rasu.
Ranar Alhamis ne ƙasar ta ƙara samun mutane 31 kuma 11 daga waje su ka shigo da ita ƙasar.
Al-Bakri ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba ƙasar za ta fitar da sharuɗɗan yin bikin babbar sallah da kuma yadda za a yi layya.
Ƙasar da ke kudancin asiya ta fitar da ƙididdigar adadin mutanen da su ka kamu da cutar da ya kai kusan 8,400.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here