Saudiya na daf yanke hukunci kan yi ko fasa Hajjin bana

0
210

Bayan da a ka ɗaga manyan tarukan al’umma a faɗin duniya,  da su ka haɗa da gasar Olympic ta duniya da za a yi a bana a Tokyo, an matsawa Saudi Arebiya lamba da ita ma ta soke Hajjin bana domin a samu a daƙile cigaba da yaɗuwar annobar COVID-19, kamar yadda Financial Times ta rawaito. 
Mahukunta na nan na nazari a kan matakai da dama inda za su bayyana matsaya a cikin mako ɗaya, wani Babban jami’i a Hukumar Kula da Hajji da Umara ne shaidawa jaridar. 
Daga 29 ga Yuli zuwa 4 ga Agusta ya kamata a fara Aikin Hajjin bana, amma har yanzu Saudiya ba ta ɗage dokar hana jigilar jiragen sama na kasa da kasa da ta kakaba tun 20 ga watan Mayu ba. 
Haka zalika Ƙasar ta fuskanci ƙaruwar waɗan da su ka kamu da cutar bayan ta sassauta dokar kulle a kwanan nan. 
Sama da mutum 119,000 ne su ka kamu da COVID-19 a ƙasar, inda mutum 893 suka riga mu gidan gaskiya, kamar yadda wata ƙididdiga daga Jami’ar Johns Hopkins ta wallafa. 
Soke Hajjin ka iya ta’azzara matsalar tattalin arziki ga ƙasar da bata fita daga matsalar da ta ke fuskanta ta faɗuwar farashin ɗanyen mai a duniya ba. 
A na tsammanin ma su shirya Aikin Hajjin za su samar wa da ƙasar dalar amurka biliyan 12 idan an yi Hajjin.
Kawo yanzu, Hukumar Kula da Hajji da Ummara bata bada amsa game da neman bahasi a kan Aikin Hajji ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here