Saudiya za ta dawo da harkokin buɗe idanu a ƙarshen watan Shawwal

0
349

Daga Mustapha Adamu
Ministan Hukumar Harkokin Buɗe Idanu, Ahmed Al-Khateeb ya ce Saudi Arebiya za ta dawo da harkokin buɗe idanu a ƙarshen watan Shawwal, daidai da 21 ga watan Yuni, bayan an samu tsaikon watanni uku sakamakon annobar coronavirus.
Ministan ya yi wannan sanarwar ne ta kafar telebijin bayan da ya jagoranci wata ganawa ta ƙungiyar ministocin buɗe idanu na ƙasashen larabawa ran Laraba.
Ya ce yanayin da a ke ciki ya ƙarawa ƙasar gwiwar cewa za ta iya dawo da harkokin buɗe idanun kuma hakan zai ƙarawa harkokin cikin gida ƙaimi.
“Wani bincike da wata hukumomin yawon buɗe idanu su ka yi ya nuna cewa kashi 80 na ƴan Ƙasar Saudiya na son amfana da harkokin buɗe idanu na ƙasar. Za mu ƙaddamar da shirye-shiryen harkokin buɗe idanu ga ƴan ƙasa kwanan nan amma sai mun haɗa kai da Hukumar Lafiya da kuma sauran ma su ruwa da tsaki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa” Saudi ta fara shirin fitar da wani tallafin kuɗaɗe da ya kai sama da dalar Amurka biliyan 61 domin tserar da harkokin cinikayya daga durƙushewa da kuma rage raɗaɗin da matsalar tattalin arziki za ta haifar.
“Bangaren harkar buɗe idanu ta cikin gida ma ta amfana daga wannan tallafin a matsayin ta na bangaren tattalin arziƙi mai muhimmanci sabo da ita ce ke ɗauke da albashin ma’ikata ƴan ƙasa har kashi 60 a babgaren ma’aikatu ma su zaman kan su har tsawon watanni 3,” in ji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here