Ba za mu yi ganganci da lafiyar alhazan Najeriya ba- NAHCON

0
7

Daga Mustapha Adamu

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta tabbatar da cewa ba za ta yi ganganci da wasarere da lafiyar alhazan Najeriya ba.

Kwamishina mai kula da aikace-aikace, lasisi da kuma ma su harkar sufurin jiragen sama ma su zaman kan su, Alhaji Abdullahi Magaji Harɗawa ya bada tabbacin yayin da ya ke amsa tambayoyi daga gidan rediyo na France da Muryar Amurka (VOA) a ofishin sa ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa, yayin da Hukumar ke jiran bayani a hukumance daga Saudiya a kan za ta yi Aikin Hajjin 2020 ko ba za ta yi ba, ita ma sai ta yi nazari a kan ya dace ta je Hajjin ko bai dace ba sabo da muhimmancin rayuka da lafiyar ƴan Najeriya.

Da a ka yi masa tambaya a kan matsayar hukumar a kan Hajjin bana duba da cewa lokaci ya fara ƙaratowa, sai ya ce hukumar na tuntubar masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasa kan yadda za a bullo da wani kundi domin ya yiwa gwamnatin Najeriya jagora wajen yanke hukunci na ƙarshe.

Alhaji Harɗawa ya yi bayanin cewa kafin mahukunta a Saudiya su dakatar da shirye-shiryen Aikin Hajji, Hukumar Kula da Alhazai ta ƙasa ta samu ragi har na Naira biliyan 3 akan farashi da tsarin jigilar alhazai a jiragen sama, lamarin da har ya sanya gwamnatin tarayya ta yabawa sabon shugabancin hukumar.

Sai dai ya yi takaicin cewa wannan ragin da a ka samu ka iya rushewa sakamakon annobar COVID-19 sabo da tsarin sufuri da gurin kwana da a ka yi a baya ka iya ɗagawa ya zama daidai da ƙa’dojin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gindaya wanda Najeriya ma ta sa hannu a yarjejeniyar.

Ya kuma tabbatar da cewa a shirye hukumar ta ke a kan ko wanne irin mataki Saudiya za ta ɗauka idan a ƙarshe ta yanke cewa za a yi Hajjin bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here