Saudiya za ta buɗe masallatai 1,560 a Makka ran Lahadi

0
5

Bayan an shafe kusan watanni uku da kulle masallatai a Birni mai tsarki na Makka sakamakon annobar COVID-19, a ranar Lahadi ne za a sake buɗe masallatai har 1,560 a birnin, amma a ƙarƙashin tsauraran matakai na kariyar lafiya.
Hukumar Kula da Addinin Musulunci ce ta bayyana cewa za a buɗe masallatan amma za a ɗauki matakan kariya da su ka haɗa da cewa sau ɗaya za a riƙa yin sallah a kan darduma sai a ɗauke sannan kuma da tabbatar ds cewa masallata sun baiwa juna isashshiyar tazara.
Hukumar ta ƙara da cewa an tanadi ma’aikatan sa kai da za su riƙa manna takarda a matsayin alama domin tabbatar da bada tazarar tsakanin masallata.
Ma’ikatan sa kan za su riƙa tuntar da masallata a kan matakan kariya sannan an manna takardu ma su ɗauke da bayanan kariya a ciki da wajen masallatan.
Haka zalika ƙasar ta ɗauki gabaran wayar da kai kan bada tazara tsakanin juna ta kafafen sadarwa na zamani a shirin da take na ɗage dokar hana shige da fice ranar Lahadin.
A tuna cewa, a kwanaki shida, har zuwa ranar Juma’a, sama da mutane 4,000 ne ke kamuwa da cutar COVID-19 a Saudiya, bayan da Hukumar Lafiya ta ƙasar ta bayyana cewa mutane 4,301 ne su ka kamu da cutar a awa 24 da wuce, sannan mutane 45 su ka rasu.
Sabuwar ƙididdiga ta nuna cewa jumullar mutane 150,292 ne su ka kamu da cutar, in da 1,184 su ka rasu a ƙasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here