Tsohon Shugaban NAHCON ya faɗi yadda za a faɗaɗa Aikin Hajji don bunƙasar arziƙi

0
441

…ya kuma ce ‘ina da yaƙinin za a yi Hajjin bana’
Daga Mustapha Adamu
Shugaban Hukumar Kula da Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Barista Abdullahi Muhammad Mukhtar ya bayyana yaƙinin sa na cewa za a yi Aikin Hajjin bana duk da yaɗuwar cutar COVID-19 a Saudiya.
A wata hira da ya yi da bangaren hausa na BBC ranar Asabar, Mukhtar ya fahimci cewa za a yi Aikin Hajjin bana amma da alhazai ƙalilan, in da hakan zai bada damar aiwatar da ƙa’idojin kariya daga cutar da masana harkar lafiya su ka bayar.
“Ina da yaƙinin in Allah Ya yarda za a yi aikin Hajji bana amma fa da alhazai kaɗan domin hakan ne zai bada damar aiwatar da ƙa’idojin da masana harkar lafiya su ka gindaya domin kariya daga kamuwa da cutar coronavirus. Da ma wasu shawarwari na mazhabobin addinin musulunci a kan sauƙaƙa aikin hajji,”
Tsohon Shugaban ya yi wannan tsokaci ne a BBC yayin da ya ke karatun digiri na biyu a kan wani maudu’i mai taken “Makoma, Damammaki da kuma Ƙalubalen da ke fuskantar tafiyar da harkar Aikin Hajji a duniya”
Da ya ke bayani a shirin, Barista Mukhtar ya lissafa hanyoyin da za a faɗaɗa da bunƙasa Aikin Hajji kamar yadda wata ma’ikatar shirye-shiryen Aikin Hajji mai suna Tabung Hajj ta Malaysia ta yi ta hanyar tsarin adashin gata, ya ƙara da cewa wannan zai kawo tagomashi a gaba ɗaya harkar Aikin Hajji.
In da ya ce wannan mai samuwa ne amma sai ta hanyar faɗaɗa ilimin harkar Aikin Hajji.
Game da alfanon da binciken na sa zai kawo, ya ce “wannan zai bawa Afirka damar yin gogayya da ƙasashen da su ka yi shura wajen Aikin Hajji kamar su Malaysia, Indonesia da Pakistan.”
A shekaru 26 da ya kwashe a harkar, Mukhtar ya yi ƙoƙarin ganin hukumomin kula da Aikin Hajji sun zama wasu kafafe na bunƙasa arziƙin ƙasashen su ba wai su tsaya da ƙafafun su ba kaɗai.
Ya ce faɗaɗa harkokin Hajji zai iya samhwa ne kawai ta hanyar yin cinikayya ta halal da kayayyakin da shari’a ta yadda, ta inda mahajjata za su amfana, in da ya bayyana cewa masu aiwatar da harkokin Hajji sai sun zage dantse sannan harkar ta ƙara bunƙasa.
“Ma’ikatun hada-hadar Aikin Hajji na gwamnati da ma su zaman kan su za su samu ƴancin kan su daga sa rai da abin da gwamnatoci za su ba su ko kuma su rika yi musu katsalandan. Hakan kuma na iya samuwa ba tare ma da an ƙara farashin Hajji ba. Har sai ta kai ga ita kan ta gwamnatin ta amfana da ribar da a ke samu ta harkar Aikin Hajji. Wannan ne ya sanya ginshiƙin binciken nawa shine Harkokin Kuɗaɗe na Musulunc

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here