Alhazai 10,000 ne za su yi Hajjin bana kuma sai an yi wa kowa gwajin Corona

0
213

Alhazan da za su yi Aikin Hajjin bana ba za su gaza dubu goma (10,000) ba a wani mataki na daƙile yaɗuwar cutar COVID-19, in ji Ministan Lafiya na Masarautar, Dakta Tawfiq Al-Rabiah ranar Talata.
A kowacce shekara, Saudi Arebiya na karbar baƙi sama da Miliyan Biyu da Rabu (2.5 million) da ke zuwa yin Aikin Hajji.
Amma a wani mataki na daƙile ci gaba da yaɗuwar annobar COVID-19 a tsakanin Alhazai, Saudiya ta yanke hukuncin yin Hajji amma ga mazauna ƙasar kawai.
A haɗin gwiwa da Hukumar Lafiya da ta Kula da Hajji da Ummara na ƙasar, Saudiya ta ce duk wanda zai yi Aikin Hajjin sai an yi masa gwajin cutar ta Coronavirus kafin ya isa birni mai tsarki.
Haka kuma ƴan ƙasa da shekara 65 ne za su yi Aikin Hajjin bana.
Duk Alhazai za su killace kan su na mako biyu bayan sun gama ibadar Hajji.
Dukkan ma’aikata da ƴan sa kai za su yi gwajin corona kafin a fara Aikin Hajjin.
Za a riƙa lura da yanayin lafiyar kowanne mahajjaci a kowacce rana.
An samar da asibiti domin yanayi na gaggawa a lokacin ibadar.
Haka zalika za a tsaurara dokar tazara da juna a lokacin aikin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here