Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta ce tana sane da duk wasu tambayoyi da neman bahasi da a ke yi mata a kan matakin da a ka daɗe a na tsimaye daga Saudi Arebiya a kan Aikin Hajjin 2020.
Sabo da haka hukumar ke tabbatar wa da al’umma cewa da zarar shugabancin hukumar ya kammala duk wasu shirye-shirye na gudanarwa, Shugaban hukumar zai yi taron ganawa da manema labarai, in da a nan ne zai amsa dukkanin tambayoyin al’umma.
A wata sanarwa daga Jami’ar yaɗa labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara, NAHCON ta ce ta na sane da tambayoyi da nuna alhini game da soke Aikin Hajjin bana ga ƙasashen ƙetare.
Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukacin shugabancin hukumar ya karbi wannan hukunci da Saudiya ta yanke a matsayin ƙaddara daga Ubangiji, ta kuma yabawa ƙasar a bisa jarumtar da ta yi.
Hukumar NAHCON na kira ga maniyyata da su kwantar da hankalin su domin za ta tsaya tsayin daka ta kare musu haƙƙoƙin su.
Ta kuma godewa al’umma a bisa addu’o’in fatan alheri da goyon baya dasu ke nuna mata