Hajj 2020: Hukumar Alhazai ta Kano ta bawa maniyyata aikin Hajji zabi biyu

0
264

-Hukumar Alhazai da jihar Kano, KSPWB ta ce za ta mayar wa dukkan maniyyata kudadensu
– Hukumar ta kuma bawa maniyattan zabin ajiye kudinsu a hannunta don aikin Hajjin 2021 –
Wannan na zuwa ne sakamakon soke aikin hajji ga maniyyatan sauran kasashen duniya da Saudiyya ta yi a bana saboda
 korona Hukumar Jin Dadin Alhazai na jihar Kano, KSPWB, ta ce a shirye ta ke ta mayar wa dukkan mutanen da suka biya kudin kujerar hajjin 2020 kudadensu. Babban sakataren hukumar, Muhammad Abba, ne ya bayar da wannan tabbacin yayin hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a ranar Alhamis a Kano.
NAN ta ruwairo cewa gwamnatin Saudiyya a baya bayan nan ta ce ba za a bari maniyyata daga wasu kasashe su tafi kasa mai tsarki don yin aikin hajjin na bana ba domin coronavirus. Amma Saudiyyar ta ce za a bari duk wani musulmi da ke zaune a kasar ya yi aikin hajjin ko da kuwa ba dan asalin kasar ta Saudiyya bane.
Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump Mr Abba ya shaidawa NAN cewa wadanda suke son a mayar musu da kudadensu za a mayar musu kana wadanda ke son ajiye kudin don hajjin shekarar 2021 suna iya barin kudinsu da hannun hukumar. Ya bayar da tabbacin cewa babu wani cikin wadanda suka biya kudin aikin hajjin da zai rasa ko da kwabo ne cikin kudinsa. A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta lissafa sharruda shida dukkan masu niyyar zuwa sauke farali a kasar mai tsarki a shekarar 2020 za su cika don yin aikin Hajjin na bana.

A yayin taron manema labarai a ranar Talata, Ministan Lafiya na Saudiyya, Tawfiq Al-Rabiah ya ce za a bawa wadanda shekarunsu bai haura 65 ba kuma masu cikaken lafiya daman zuwa sauke faralin. Ya kara da cewa kuma za a yi wa maniyyatan gwajin coronavirus kafin a bari su shiga kasa mai tsarkin kuma za su kwashe kwanaki 14 a killace a masaukinsu bayan kammala aikin hajjin.
Ministan lafiyar ya kuma bayyana cewa an tanadi matakai don ganin maniyyatan sunyi aikin hajjin a yanayin bayar da tazara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ya ce za a kayyade adadin maniyyatan da za suyi aikin hajjin kuma akwai yiwuwar ba za su wuce 10,000 ba. “An tanadi asibitoci a wurare da dama saboda yiwuwar samun wadanda ke bukatar taimakon gaggawa baya ga cibiyar lafiya da ke Dutsen Arafat,” in ji shi. “Likitoci da motoccin asibiti za su rika yawo tare da maniyyatan a yayin da suka ibadojinsu. “Munyi shiri na musamman domin aikin Hajjin bana. “Za ayi aikin Hajjin cikin lafiya a kare lafiya,” in ji shi
Source: Legit

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here