Hajj 2020: Alhazan Kwara na tsimayen matakin da NAHCON za ta ɗauka

0
481

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ce tana tsimayen matakin da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) za ta ɗauka a kan Hajjin 2020.
Babban Sakataren hukumar, Alhaji Tunde Jimoh ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Ilorin ran Juma’a.
Ya yi bayanin cewa dole kowa ya rungumi ƙaddara a kan matakin da soke Aikin Hajji ga ƴan ƙasashen waje da Saudi Arebiya ta ɗauka.
Babban Sakataren ya  ƙara da cewa Saudiya ta ɗauki matakin ne a yaƙin da ta ke da annobar coronavirus da ta addabi duniya.
Alhaji Jimoh ya bayyana cewa da zarar NAHCON ta bayyana matsayar ta, to hukumar ba ta da wani zabi illa ta aiwatar da matakin domin amfanin mamiyyatan Jihar Kwara.
Ya kuma yabawa maniyyatan Jihar a bisa hakuri da juriya da su ka yi, da kuma Malaman Addinin Musulunci da su ke ta addu’a kan annobar coronavirus

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here