Harkokin sufuri sun koma sabon gurin jiran matafiya na filin jirgin saman Jeddah

0
211

Dukkan harkoki a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Sarki  Abdulaziz sun koma sabon gurin jiran matafiya. Dukkan harkokin sauka da tashin jirage sun koma bangaren.
A tuna cewa Sarki Salman ne ya ƙaddamar da bangaren a watan Satumbar bara. Tun a watan Mayun baran ake harkoki a guraren jiran matafiya daban-daban a filin jirgin.
Daga yanzu a sabon gurin jirage za su riƙa sauka da tashi, in da a ka yiwa filin jirgin saman gini da ya dace da zamani. Shi ne kuma filin jirgin sama ma fi girma a yankin larabawa.
An gina filin jirgin a kan fili mai yawan murabba’i 810,000 in da  filin ka iya ɗaukar har matafiya miliyan 30 a shekara.
Haka kuma filin jirgin na ɗauke da bangaren jirgin ƙasa na tafi-da-gidan-ka in da ba kasafai a ke samun haka a duniya ba. Da jirgin ƙasan ne za a riƙa ɗaukar matafiyan da su ka kammala shirye-shiryen tafiya zuwa wajen hawa jirgi sannan a dawo da su idan jirgi ya sauka.
An samar da kantoci 220 da kuma guraren harkokin tafiye-tafiye ga kamfonin jigilar jirage har 80

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here