Wakafi (Sadaukar Da Dukiya Domin Allah) A Musulunci, Daga Imam Murtadha Gusau

0
197

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkkaken Sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyan halitta, Annabin karshe, Annabi Muhammad (SAW), da alayensa da sahabban da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Ya ku ‘yan uwa na Musulmi masu daraja, masu albarka, a yau zan yi magana In Allah yaso akan wani muhimmin al’amari da ya kamata dukkanin Musulmi su sani, kuma su fahimce shi yadda ya kamata, sannan kuma suyi aiki da shi, wannan kuwa shine WAKAFI, wato sadaukar da amfanin wata dukiya ko kaddara, domin amfanin al’ummah baki daya.
Ya ku al’ummah, wannan maudu’i na yin magana akan wakafi muhimmi ne sosai matuka, amma saboda rashin mayar da hankali a gare shi, shi yasa ba kowa ne yake kokarin aiwatar da shi ba domin ya gyara lahirar sa da kuma taimakon al’ummah.
1. Menene ma’anar wakafi?
Ma’anarsa a harshen larabci da kuma wurin malaman fikhu shine: Idan an ce Al-wakfu, an samo shi ne daga wakafa, jami’insa kuwa shine Aukaf, ana cewa ya tsaida abu, kuma ya kiyaye shi, kuma ya bayar da shi. Duk ma’ana daya ce. Amma a wurin malaman fikhu: Shine tsare asalin abu, tare da bayar da sadakar amfaninsa.
2. Asalin yadda aka shar’anta wakafi:
Wakafi Sunnah ce tabbataciya daga Manzon Allah (SAW), haka kuma ijma’i ne na malamai. Amma abin da ya tabbata a Sunnah shine Hadisin da yazo cikin Bukhari da Muslim cewa, lallai Umar Allah ya kara masa yarda, yace:
“Ya Manzon Allah! Lallai na samu dukiya a Khaibar irin wadda ban taba samun irin ta ba a rayuwa ta, meye za ka umurce ni da in yi da ita? Sai Ma’aikin Allah (SAW) yace: “In ka so ka tsare asalin ta, kayi sadaka da ita ba tare da an sayar da asalin ta ba, kuma ba za’a kyautar ba, kuma ba za’a gada ba.” [Bukhari, Muslim, Tirmizi, Nasa’i, Abu Dawud, Ibn Majah da Ahmad ne suka ruwaito].
Sai Umar ya sadaukar da ita ga talakawa da ‘yan uwa na kusa da bayi da kuma saboda daukaka addinin Allah da matafiya da kuma baki. Kuma babu laifi ga wanda yake kula da ita da yaci daga ciki ba tare da yin barna ba.
Kuma wakafi yana cikin abubuwan da suka kebanci Musulumi ne kawai, Jabir Allah ya kara masa yarda, yace:
“Babu wani daga cikin Sahabban Manzon Allah (SAW) da yake da iko face sai da yayi wakafi da dukiyarsa. Kuma wannan yake bayyana muna cewa, abin da mutane ke kansa yanzu shine akasin abin da aka sani a zamanin Sahabbai. Da yawan mutane yanzu babu abin da suka sani sai wasiyah, ba su san wakafi ba.”
3. Hikimar shar’anta wakafi:
• An kwadaitar ga duk wanda Allah ya yalwata masa dukiya daga cikin masu kudi da su kara biyayya ga Allah ta hanyar yawaita yin da’a gare shi, kuma su yawaita neman kusanci ga Allah ta hanyar ware wani abu na dukiya tsayayya, abin da asalin sa zai dawwama, kuma anfanin sa yaci gaba, domin tsoron kada dukiyar ta koma hannun wadanda ba za su iya kulawa da ita ba bayan rasuwa, kuma ba zai iya kiyaye wa ba, sai ya share ayyukansa don kar ya wayi gari a karshe ‘ya’yan nasa su zama cikin wadanda za’a taimaka masu saboda fatara, domin kaucewa wadannan hasashen da kuma tarayya a cikin aikin alheri aka shar’anta wa mutum yayi wakafi a lokacin rayuwarsa, domin mai wakafin yasa ido da kansa, kuma ya sanya shi a wurin da yake so ya sa shi da kansa, ya kuma jibinci kulawa da shi, da ci gaba da bada alheransa bayan ya rasu kamar yadda yake yi a lokacin yana raye.
• Babban su shine babban abinda ya sanya tsayuwar Masallatai da makarantu, da kamanta haka na ayyukan alheri da kuma kiyaye su, domin mafi yawan Masallatai a tsawon tarihin Musulunci sun samu ne wurin wannan wakafi, kai sai da ma ta kai duk abunda Masallaci yake bukata, shimfida ne, da tsaftacewa, da tallafi da ake ba masu kula da shi, duk bai gushe ba ana karfafarsa ne daga wakafi.
4. Lafuzzan da ake amfani da su wurin bayar da wakafi:
Wakafi na da lafuzza bayyanannu ga su kamar haka:
• Na bayar da (abu kaza) a matsayin wakafi.
• Na tsare shi daga magada na.
• Na bayar da shi fisabilillahi.
Amma lafuzzan kinaya a wurin aiwatar da wakafi, sune kamar haka:
• Na bayar da sadaka.
• Na haramta wa kaina shi.
• Na bayar da shi har abada.
Sannan lafuzzan kinaya suna kasancewa ne da daya daga cikin abubuwa uku kamar haka:
• Niyyah: Idan yayi furuci, kuma yayi niyyah da daya daga cikin wadannan lafuzzan kinaya to ya zama wakafi.
• Idan lafuzzan suka yi kusanci da daya daga cikin lafuzza bayyanannu, ko na kinaya, kamar na sadaukar da wani abu a matsayin wakafi da sauran su.
• Ko kuma ya siffanta wani abu tabbatacce na kaddararsa da siffofi kamar haka: yace (Abu kaza) ya haramta (a gare ni), ba’a sayarwa kuma ba’a kyautarwa, kamar yadda muka bayyana a halin kinaya da sauran su, kuma yana tabbata ta hanyar ayyuka, kamar mutum ya gina Masallaci a cikin filinsa, sannan ya kira mutane zuwa a yi Sallah.
5. Nau’ukan wakafi:
Wakafi ya rabu ta fuskar da aka lura da shi kamar fuskar farko wadda ta sanya shi nau’i biyu:
• Khairy.
• Ahly.
Wakafin Khairy: shine wanda za’a yi wakafi tun farkon lamari akan fuskar alheri ko da kuwa lokaci ne kayyadadde, sai bayan haka ya kasance wakafi ga mutum sananne ko mutane sanannu, kamar yayi wakafi da filinsa ga asibiti ko makaranta, sannan bayan haka ga yaran sa, su dauka daga baya.
Wakafi Ahly ko na zuri’a: shine wanda za’a yi wakafi tun farkon lamari ga wani mutum sananne ko wasu mutane sanannu, sai kuma a sanya karshen sa alheri ne kamar ya sanya shi ga kansa, sannan ‘ya’yansa, sannan a bar shi ga ayyukan alheri.
6. Abuwan da ake yin wakafi da su:
Akwai dukiya tabbatacciya wadda za’a iya kimanta ta, kamar fili ko gida, wannan duk Malamai sunyi ijma’i a kansa. Ko wanda za’a iya dauka kamar; littattafai da tufafi, dabbobi da kuma kayan yaki. Domin fadin Manzon Allah tsira da ammincin Allah su tabbata a gare shi:
“Amma Khalid, to lallai ku kuna zaluntar Khalid, lallai shi ya tsare sulkensa na yaki kuma ya tanadar da shi ne saboda ayyukan daukaka Kalmar Allah.” [Bukhari]
7. Sharuddan wakafi:
Anyi sharadi ga wanda zai yi wakafi cewa, dole sai ya dace da shari’ah. Idan ya dace da shari’ah to yayi, idan kuma bai dace ba to bai yi ba.
• Ya kasance ya cancanci bayarwa, ba na fashi ba ne, ba kuma ya saya ba ne amma bai karba ba domin ya mallake shi tabbatacciyar mallaka ba.
• Ya kasance wanda zai yi wakafi mai hankali ne. Ba ya halatta wakafin mahaukaci ko mara wayo da sauran su.
• Ya kasance ya balaga, ba ya halatta wakafin karamin yaro, daidai ne, ya kasance mai wayo ne ko mara wayo.
• Ya kasance mai lura, wakafi ba ya halatta ga wanda yake wawa ko gafallale ko dukan shaho.
8. Sharuddan abubuwan da za’a yi wakafi da su:
Domin wakafi ya kasance wanda za’a zartar akan abinda aka yi wakafin don haka aka shardanta wadannan sharudda kamar haka:
• Ya kasance dukiya ce tsayayya, kamar gida ko waninsa.
• Ya kasance an iyakance abun da aka yi wakafi da shi.
• Ya kasance abunda aka yi wakafi da shi an mallake shi lokacin da aka yi wakafin.
• Ya kasance abunda aka yi wakafi da shi sananne ne, domin ba’a yin wakafi da abunda ba’a sani ba.
• Ya kasance abunda za’a yi wakafi da shi babu hakkin wani a ciki.
• Ya kasance zai amfanar idan aka yi wakafi.
• Ya kasance amfanuwar abun wakafin ta halatta.
9. Yadda za’a amfana da abun da aka yi wakafi da shi:
Ana iya amfana da abin da aka yi wakafi da shi kamar gida ko abun hawa da sauran su.
10. Banbanci tsakanin wakafi da wasiya:
• Lallai shi wakafi, yana tsare asalin dukiya ne, da kuma bada sadakar amfanuwar. Wasiya kuma ita ce, mallakar da abun amma bayan mutuwa, ta hanyar bayarwa ne a abunda ya kasance ga shi kuru-kuru ko kuma amfanarwa ne.
• Wakafi yana lizimtar mutum, kuma ba’a maida shi (wato ace an fasa) a fadin Malamai ba’abota ilimi, domin fadin Manzon Allah (SAW) ga Umar Allah ya kara masa yarda:
“Idan ka so sai ka tsare ta kayi sadakar asalinta. Sai kuma yayi sadakar.”
Amma wasiyyah tana lizimta, kuma yana halatta ga wanda yayi wasiyyah ya janye wasiyyar, ko kuma wani sashi na ta.
• Wakafi yana fitar da mallakar ainihin dukiya daga wanda ya bada ita zuwa ga wani, sai dai tana kebanta ne ga abun da ake amfanuwar sa da wakafin.
Ita kuwa wasiyyah tana sa mallakar ainihin dukiya ne ga wanda aka yi wa wasiyyah. Ko amfanin ta yana komawa ne ga wanda akayi wa wasiyyar.
• Mallakar da amfanuwar wakafi hukuncinsa yana bayyana ne a lokacin da me wakafin yake raye da kuma bayan ya mutu. Shi kuma mallakar da wani abu a wasiyyah ba ya bayyana sai bayan mutuwar wanda yayi wasiyyah.
• Wakafi ba ya da haddi akan mafi yawansa, ita kuwa wasiyyah ba ta wuce daya bisa uku na dukiya akan kayan gado.
• Wakafi yana halatta ga wanda zai ci gado, wasiyyah kuma ba ta halatta ga wanda zai ci gado, sai idan sauran magada sun yarda.
Ya ku ‘yan uwa na masu girma, daga karshe wannan shine dan abun da ya sawwaka game da bayani akan wakafi. Ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bamu ikon aiwatarwa, amin.
Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka a koda yaushe.
Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah, Muhammad (SAW).
Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi a cikin dukkanin abun da yake damun mu, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here