Adamawa: An shawarci maniyyata da su ci gaba da ajiye kuɗin su zuwa Hajjin 2021

0
7

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Adamawa, Mallam Salihu Abubakar ya shawarci maniyyata Aikin Hajji na jihar da su bar kuɗaɗen su da su ka biya domin zuwa Hajjin 2021.
Amma kuma Shugaban, wan da shine kuma Sakatare na din-din-din a hukumar, ya ƙara da cewa duk mai son ya karbi kuɗin sa, to ƙofa a buɗe take da ya je hukumar ya karba.
Wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar mai ɗauke da sa hannun sa ta ce shugaban ya yi wannan bayani ne lokacin da ya kaiwa Gangwarin Ganye, Alhaji Adamu Ummaru Sanda ziyara a fadar sa.
Sanarwar ta ce ” Bayan Saudi Arebiya ta soke yin Hajjin bana ga ƙasashen waje sakamakon yaɗuwar annobar COVID-19, Mallam Abubakar na kai ziyara  ga maniyyatan Jihar a ɗaukacin ƙananan hukumomi 21 na jihar,  domin ganawa da su da kuma ba su shawara a kan su bar kuɗaɗen su da su ka biya zuwa Hajjin baɗi. Amma waɗan da su ke so a dawo musu da kuɗaɗen na su, to za su iya neman haƙƙin su

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here