Hajjin 2020: An Baiwa Maniyyatan Kano Zabi Kan Kuɗin Ajjiya.

0
8


Daga Jabiru Hassan, Kano
Hukumar Kula da jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta baiwa maniyyatan da su ka bada kuɗaɗen ajjiya ga hukumar zabin karbar kuɗin su ko kuma su yi haƙuri sai Aikin Hajjin 2021.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi  ce ta sanar da hakan a ganawar ta da wakilin mu ranar Alhamis.
 Ta ce hukumar ta bi sahun takwarorin ta na sauran jihohi wajen shirin maidawa maniyyata kuɗaɗen da su ka ajjiye domin tafiya  Hajjin bana ba tare da tsaiko ba.
Haka kuma hukumar za ta ci gaba da ajjiye kuɗaɗe na maniyyata da su ka amince za su bar kuɗin su zuwa baɗi.
Ta ƙarsla da cewa, musamman ganin cewa wannan lamari ya shafi duka duniya ne sabo da annobar Covid-19 wanda hakan ta sanya ƙasar Saudiyya ta soke Aikin Hajjin bana ga ƙasashen waje domin tabbatar da daƙile cutar baki ɗaya.
Hajiya Hadiza ta bayyana cewa Hukumar jin ta yi godiya ta musamman ga ɗaukacin maniyyata da su ka himmatu wajen bada kuɗin su na ajjiya, sannan tana mai  jaddada cewa da yardar Allah maniyyata za su ci gaba da samun kulawa ta musamman daga hukumar kamar yadda aka saba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here