Hajjin 2020: Tambuwal ya umarci Hukumar Jin Daɗin Alhazai da ta dawowa maniyyata kuɗaɗen su

0
481

Gwamnan Jihar Sokoto, ya umarci Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar da ta dawowa da maniyyata kuɗaɗen Aikin Hajji da su ka biya.
A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Daily Trust, Shugaban hukumar, Shehu Muhammad Dange ya bayyana cewa Gwamnan ya umarce su da su fara shirye-shiryen maidowa da waɗan da su ka biya kuɗaɗen ajiya na Aikin Hajjin bana haƙƙunan su.
Ya ce”mun umarci Jami’an Aikin Hajji na Ƙananan Hukumomi da su tattara bayanan da ke gaban su, sai su kawo hukumar domin kada a samu matsala.
Dange ya bayyana cewa gurbin mutane 4,000 Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta baiwa jihar kafin Saudi Arebiya ta soke Aikin Hajji ga Ƙasashen waje, in da ya ƙara da cewa ƙara da cewa duk wanda ya ke buƙatar a dawo masa da haƙƙin sa to za a yi hakan ne daidai da sharuɗɗan da NAHCON ɗin ta gindaya.
Ya ce”amma na san akwai maniyyatan da za su so su ajiye kuɗaɗen nasu zuwa baɗi. Ina kira ga al’umma da su ɗauki wannan yanayi a matsayin ƙarddara,”
A tuna cewa Ƙasar Saudiyya ce dai ta soke yin Hajji ga ɗaukacin ƙasashen duniya kamar yadda ta saba sakamakon yaɗuwar annobar COVID-19, lamarin da ya sanya jihohi a Nijeriya su ka fara ɗaukar gabaran maidawa maniyyata kuɗaɗen da su ka ajiye

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here