Soke Hajjin bana ya janyo wa kamfanonin jiragen sama asarar N50b

0
180

An yi ƙiyasin cewa kamfanonin sufurin jiragen sama sun tafka asarar da ta kai sama da naira biliyan 50 sakamakon matakin da Saudi Arebiya ta ɗauka na soke Aikin Hajji ga ƙasashen waje, in da hakan ya kawo musu naƙasu wajen shigowar kuɗaɗe a shekarar nan.
Yayin da ma su ruwa da tsaki a harkar hajji su ka rungumi ƙaddara sakamakon soke hajjin da Saudiyya ta yi domin daƙile yaɗuwar annobar COVID-19, su kuwa kamfanonin jiragen sama matakain ya haifar musu da ɗa mara ido.
Soke hajjin ya ƙara ta’zzara matsalolin da kamfanonin jigilar jiragen sama. 
Daily Trust ta rawaito cewa kamfanoni uku ne da su ka haɗa da Max Air, Med-View da Sky Power su ka yi jigilar Aikin Hajjin 2019.
Amma a bana, lokacin da Hukumar Kula da Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta tallata gurbin jigilar Hajjin bana ga kamfanoni ma su sha’awa, kamfanoni 7 ne su ka nuna sha’war su ta yin jigilar alhazan. Kamfanonin sun haɗa da Max Air, Azman, Arik, Med-View, Sky Power da kuma kamfanoni biyu na Saudiyya wato FlyNas da Sky Prime.
Tabbas soke hajjin zai kawo wa waɗannan kamfanoni asar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here