Hajjin 2020: Saudiya za ta maido da kuɗaɗen aikace-aikace a Satumba

0
377

Daga Mustapha Adamu
Shugaban Hukumar Hajji ta Ghana, Sheikh I.C. Quaye da Shugaban Ƙungiyar Wakilan Hajji ta Ghana sun ce sun samu tabbaci daga Hukumar Hajji da Umarah ta Saudi Arebiya  za ta fara maido da kuɗaɗen da a ka bata na aikace-aikacen Hajjin 2020.
A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da shugabanni biyun su ka fitar ranar Juma’a sun bayyana cewa maniyyatan ƙasar sun nemi su maida mu su da kuɗaɗen Hajji da su ka biya, inda su ka tabbatar da cewa za su dawowa da kowa kuɗin sa da zarar Saudiya ta maidowa ƙasar na ta kuɗaɗen da ta bayar na aikace-aikace.
Sanarwar ta yi bayanin cewa lafin bullar annobar coronavirus, Hukumar Hajji ta riga ta biya kuɗaɗen aikace-aikace ga Saudiya, da su ka haɗa da kuɗaɗen kama masauki, sufuri, abinci da sauran su domin alhazan Ghana su yi Aikin Hajji cikin sauƙi.
“Mun karbi sanarwa daga Hukumomin Saudiya cewa za su fara shirin maido da 
Kuɗaɗe daga watan Satumbar 2020 bayan da ta yanke yin Hajji ga ƴan ƙasa kawai,” in ji sanarwar.
“Muna kira ga maniyyata da su ka biya kuɗaɗen su kai tsaye ko ta Hukumar Hajji ko ta banki da su yi haƙuri su bawa hukumomi haɗin kai domin ana iya bakin ƙoƙari a share musu hawayen su,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here