Maganin Farin Jini Daga Bakin Manzon Allah (SAW)

0
3907

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkanin kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabin mu, Muhammad (SAW), da iyalansa da sahabbansa baki dayansu. Bayan haka:

Ya ku bayin Allah, wani Sarki ne wata rana ya fita kilisa da mutanensa da fadawansa, sai ya iske wani tsoho tukuf-tukuf yana shukar dabino. Sai Sarki yace a tsaya. Yasa aka kira tsoho, tsoho yazo yayi gaisuwa. Sarki yace tsoho:

“Wannan shuka taka ba ta makara ba kuwa? Yaushe har wannan dabino zai girma, har yayi ‘ya ‘ya kaci?”

Tsoho yace Allah ya taimaki Sarki:

“Ko ni ban ci ba ai na baya na za su ci. Mu dabinon da muke ci yanzu ba kakanninmu ba ne suka shuka suka bari, mu muke cin amfaninsa a yanzu? Mu ma ai ya zama dole mu shuka domin mu bar wa na baya, matukar muna son alkhairi ga kawunan mu.”

Sarki yaji dadin wannan magana ta tsoho yace:
“Gaskiyar ka tsoho.”

Sarki ya dubi shamaki yace ayi masa kyauta. Shamaki ya dauko dukiya ya bai wa tsoho. Tsoho ya fadi gaban Sarki yayi godiya yace:

“Ikon Allah, ranka ya dade, dabino shekara da shekaru ya kan yi kafin ya haihu amma ka ga ni nawa dabinon tun ban gama shuka shi ba yayi ‘ya ‘ya.”

Sarki yayi murmushi ya sake duban shamaki yace a kara masa. Tsoho ya karba ya sake godiya yace:
“Allah ya ja zamanin Sarki, duk girman dabino sau daya yake yin ‘ya ‘ya a shekara, amma nawa yanzun nan gashi har ya haihu sau biyu.”

Sarki yace a kara masa kyauta. Ana ba shi tun bai yi magana ba sai waziri ya dubi Sarki yace:
“Ranka ya dade, gara fa mu wuce mu bar wannan tsoho don sai ya kare duk abin da aka fito dashi da iya bakin sa.”

Sai tsoho ya dubi waziri yace:
“Ba iya baki ba ne, so nike da Sarki da mutanensa da sauran al’ummar duniya su fahimci cewa, ba’a makara da shuka alkhairi.”

Darasi a cikin wannan labari:
Akwai karantar wa akan cewa lallai abunda al’ummah ta ke son samu na ci gaban ta a can gaba, to tun a baya ne ta ke shuka shi. Sannan akwai yin kira game da alfanun da ke tattare da yin kyauta da shuka alkhairi, tare da kuma nuna munin rowa da marowata a cikin al’ummah.

Ya ku ‘yan uwa, mu yawaita kyautatawa da yin alkhairi, domin alkhairi yana kara dankon zumunci, yana kara soyayya, yana tara wa mutum dimbin masoya da magoya baya. Alkhairi yana sada zumunci. Alkhairi yana hana sharri, kuma yana tunkude sharrin makiya da mahassada da makircinsu. Alkhairi yana daukaka darajar mutum duniya da lahira. Alkhairi yana kara arzikin mutum. Alkhairi yana hana kiyayya. Alkhairi danko ne, baya faduwa kasa banza…etc, don haka mu yawaita alkhairi, mu guji rowa, domin rowa tana da hadari mai yawa a rayuwar dan Adam, kuma tana da mummunan tasiri ga mai yin ta!

Annabi (SAW) ya kasance yana yiwa hatta makiyinsa kyauta da alkhairi, har ya zamanto daga karshe, makiyin nan ya ji cewa baya da masoyin da ya kai Manzon Allah (SAW) a duniya, saboda kyautatawar da yake yi masa, da kuma yawaita alkhairin sa. Hatta makiya sun tabbatar da cewa, Annabi Muhammad (SAW) yana yin kyauta, irin kyautar mutumin da baya tsoron talauci. Kuma mu ga shi kullun muna ikirarin cewa mu mabiyansa ne kuma mu masoyansa ne. To anan ina biyayyar ‘yan uwa? Ina soyayyar ta ke? Ta yaya za’a yi marowaci ya zama masoyin Manzon Allah (SAW)? Ta yaya za’a yi kuma ya zama mabiyinsa? Kun ga wannan ba zai yiwu ba ko?

Sannan Manzon Allah (SAW) yace:
“Kuyi kyauta za’a so ku.”

Sannan ya sake fada a wani Hadisin cewa:
“Hannun da yake bayar wa shine a saman hannun da yake karba a koda yaushe.”

Ya ku ‘yan uwa, wadannan Hadisai sun karantar da mu cewa, lallai duk mai yin kyauta da yawaita alkhairi, wallahi za’a so shi, sannan kuma ba zai taba yin kasa ba, kullun zai kasance a sama ne da ikon Allah.

Ya ku jama’ah, ku sani, wallahi rowa ba ta da kyau, kuma tana jawo wa mutum mummunan bakin jini, da yawaitar makiya da mahassada. Sannan rowa tana hana kofofin alkhairi su bude wa mutum, ta mayar da shi baya, yaki ci gaba a rayuwar sa, kullun ya ta yin baya. Allah ya sawwake, amin.

Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (Allah Ya kara masa yarda), yace:

“Wani mutum yazo wurin Manzon Allah (SAW) yace, “Ya Ma’aikin Allah, wace irin sadaka ce ta fi?” Sai Manzon Allah (SAW) yace, “Ita ce wadda ka bayar a lokacin da kake lafiyayye, kuma kana kankame da dukiya (wato kana tsumulmularta), kana tsoron talauci, kana sa ran zama attajiri! (ita ta fi). Yace kada ka yi jinkiri har sai ka kusa mutuwa ka rika cewa, “Wannan a kai wa wane da wane; waccan a kai wa wane da wane.” Alhali ta kai lokacin da ta zama dukiyar wane da wane!” [Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin]

Kuma sannan abu ne sananne cewa, babu yadda za’a yi wanda yake bayar wa ya rasa, da izinin Allah, domin Annabi Muhammad (SAW), mai gaskiya kuma abun gaskatawa. Wanda ba ya magana da son zuciyarsa, kuma duk abunda ya fada wahayi ne daga wurin Allah, yace:

“Ku tausayawa bayin Allah da suke a bayan kasa, ku kuma Allah da yake sama sai ya tausaya naku.”

Wannan ya nuna kenan matukar kana taimakawa bayin Allah, kana tausaya masu, kana yi masu kyauta da alkhairi, to da ikon Allah kai ma Allah ba zai manta da kai ba.

To ko bature ma me yace? Ba cewa yayi “GIVERS NEVER LACK” ba? Ka ga wannan magana haka take ko Dan uwa?

To saboda haka ni ban ga yadda za’a yi mai bayarwa ya rasa ba, sai fa idan wata jarabawa ce ta zo daga wurin Allah, wadda yayi nufin jaraba bawan sa da ita, to sai muce wannan kuma wani al’amari ne daban. Sannan haka kuma ban ga yadda za’a yi marowaci ya rabu da talauci da damuwa ba, domin da rowa da talauci Dan Jumah ne da Dan Jumai, babu yadda za’a yi ka iya raba su. Duk inda rowa tayi katutu, to zaka tarar talauci da rashin wadatar zuci sun yi kaka-gida, kuma sun samu gindin zama a wurin.

Daga cikin abubuwan da Allah da Manzon sa (SAW) suka ki, suka kyamata, kuma suka haramta, akwai rowa. Ayoyin Alkur’ani da Hadisai masu tarin yawa sun tabbatar da hakan, wanda yanayin lokaci ba zai bani damar kawo wa ba. Kai hatta Malaman Musulunci ma sun yi rubuce-rubuce akan yabon masu kyauta, masu alkhairi, da kuma suka akan masu rowa wato ذم البخل. Don haka yaku jama’ah, ya kamata mu fahimci cewa rowa bala’ice kuma masifa ce. Kuma duk wanda yake marowaci, zaka tarar jama’arsa ma duk sun watse masa, sun guje shi, domin ai kuda basa bin mai kayan gawayi. Mai bayarwa kuwa, kullun ba zaka raba gidansa da al’ummar Annabi Muhammad (SAW) ba. Allah yasa mu dace, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761

Lahadi, 05/07/2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here