Kashi 70 na baƙi, kashi 30 na ƴan ƙasa ne za su yi Hajjin bana

0
446
NIGERIA PILGRIMS MINA GOOD

Yayin da Ma’aikatar Hajji da Umara ta Saudi Arebiya ranar Litinin ta fara yin rijistar waɗanda suke da sha’war yin Aikin Hajjin bana, daga cikin mutane 10,000 da za su yi aikin, kashi 70 baƙi ne da ke zaune a ƙasar, inda kashi 30 kuma ƴan asalin ƙasar ne za su yi Ibadar.

Saudiya ta yanke shawarar yin Aikin Hajji  amma ga mutum 10,000 kawai da suje zaune a ƙasar sakamakon annobar COVID-19.

Isasshiyar lafiya ce babban matakin barin mutum ya yi Aikin Hajjin bana. Daga ƴan asalin ƙasar kuwa, za a zabo ma’aikatan lafiya ne da su ka kamu su ka kuma warke daga coronavirus, inda za a duba jerin sunayen waɗanda cutar ta kama a rumbun ajiye bayanan waɗanda su ka warke kuma su ke da cikakkiyar lafiyar yin ibadar.

Za a yi hakan ne a wani mataki na jinjina a bisa irin namijin ƙoƙarin da su ka yi na taimakon al’umma yayin yaƙi da annobar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudi Press Agency ya rawaito ta bakin Ma’aikatar.

A sanarwar da ta fitar, Ma’aikatar ta ce za a buɗe shafin yin rijista na baƙi mai adreshin www.localhaj.haj.gov.sa ranar Litinin sannan a rufe ranar Juma’a, 10 ga watan Yuli, sannan ranar Juma’a a saki sakamakon tantancewa na yin Aikin Hajjin.

Za a auna cancantar baƙi fa za su yi Aikin Hajjin ne ta yin amfani da sharuɗɗan kariya daga coronavirus.

Baƙi daga shekara 20 zuwa 50 kuma ba su da wasu muggan cutuka a jikin su suka cancanta su yi rijista. Waɗanda za su aika neman yin Hajjin sai sun tabbatar da basu da ciwon siga, hawan jini, ciwon zuciya da kuma ciwon sarƙewar numfashi, ko kuma basu kamu da coronavurus ko nuna alamun ta ba. Kuma sai sun yi gwajin lafiya da kuma nuna shaidat gwajin.

Mai yin rijistar sai ya rantse ta kafar internet cewa bai taba yin hajji ba kuma sai ya killace kan sa na tsawon kwanaki 14 kafin hajji da kuma wasu kwanaki sha huɗun bayan hajji.

Kuma sai su riƙa tuntubar Hukumar Lafiy ta ƙasar a kai a kai ta wayar salula daidai da ƙa’idojin lafiya da hukumar ta amince da su.

Haka kuma ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa za ta soke duk wani wanda yai rijista amma bai bi sharuɗɗan lafiya ba ko ya bada  bayanan ƙarya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here