Bayan da Saudi Arebiya ta soke Hajjin bana ga ƴan ƙasar waje Kwamitin Hajji na Telangana ta fara shirye-shiryen maidowa da maniyyatan da suka nema kudaɗen su da fasfunan su.
Wata majiya daga kwamitin ta ce an aikawa maniyyatan saƙon kar ta kwana domin sanar da su cewa za a dawo mjsu da fasfunan nasu.
Waɗanda suka nemi su karbi fasfunan nasu za su iya zuwa ofishin Kwamitin Telegana wanda yake a harabar Gidan Hajji daga ƙarfe 11 zuwa ƙarfe 3 na yamma.
Ana dawo da sahihan fasfunan ne ga kai tsaye ga maniyyatan da suka nema ko kuma ta wani wanda aka ɗorawa alhakin karba amma sai sun nuna sheda. Sannan fasfuna 100 ake rabawa a rana.
A wani fannin kuma ƙasar Saudiya ta buɗe yin rijistar Hajjin ranar Litinin