An tantance ƴan ƙasashe 160 masu neman yin Hajjin bana, an fara zaba daga cikin su

0
351

An kammala tantance neman yin Aikin Hajjin bana da ƴan ƙasashe 160 suka aika ta amfani da na’ura mai ƙwawƙalwa, inda tuni a ka yi nisa wajen zaben waɗan da suka cancanta, in ji Hukumar Kula Da Hajji da Ummara a ranar Lahadi.

An shirya neman ne ta amfani da cikakkiyar hanyar kariyar lafiya domin kariyar mahajjata.

Ranar 10 ga watan Yuli aka rufe aika neman kuma babban natakin yin hajjin shine cikakkiyar lafiya.

A cikin Alhazan da za a ɗauka, kashi 70 daga cikin su ba ƴan ƙasa bane inda ƴan ƙasa suka ɗauki kashi 30.

A wani bangaren kuma, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiya ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama ya shiga guraben da ake Aikin Hajji (Minna, Muzdalifa da Arafat) ba tare da izini ba daga 28 ga watan Dhul Qadah zuwa ƙarshen 12 ga Dhu Al-Hijja to za a ci tarar sa Riyal 10,000.

Za a ninka tarar idan mutum ya maimaita laifin. Ta kuma ƙara da cewa jami’an tsaro zasu kafe sanarwar a kan tituna domin a tabbatar da cewa duk wanda ya karya dokar za a tsayar da shi a hukunta shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here