Sabon tsarin shiga Harami: Za a riƙa hango Ka’aba mita 300 daga ƙofa

0
328

Aiki ya ci gaba domin kammala ginin ƙofar shiga Babban Masallacin Harami mai suna Ƙofar Abdul Abdulaziz.
Ƙofar, wacce aka ƙera ta da ado mai ɗaukar ido irin na al’adar Musulnci zai bawa masallata damar hango ƙayataccen ginin Ka’aba tun daga mita 300 wajen shigowa.
Anas Sairafi, wanda shine wakilin kamfanin zane-zanen gine-gine na Jabal Omar kuma shine Shugaban kwamitin ginawa da siyar da gidaje a Hukumar Kasuwanci  da Masana’anta ta Makka, ya ce sabon tsarin da aka yi, wanda ba a taba yin irin sa ba a baya, zai bada damar a riƙa hango cikin harami yayin da aka ƙaddamar da ci gaba da aikin sauran bangarorin masallacin ranar Juma’a.
Ya yi bayin cewa ƙofar Abdulaziz ɗin ita ce ƙofa mai lamba da ɗaya a jerin ƙofofin Harami daga bangaren kudu na masallacin.
“An tsara ƙofar ne da zane mai kyau irin na al’adun musulunci kuma an yi ta ne da fasahar zamani, inda ake ta ginin nata da kayan aiki masu inganci. An matsar da ƙofar tsawon mita 50 daga inda take na asali.”
Sairafi ya ce tsawon ƙifar ya kai mita 51, in da tsayin ƙyauren ya kai kimanin mita 20. An kuma ƙara tsayin hasumiyoyi buyu na ƙofar daga mita 90 zuwa mita 137

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here