Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai jinkai
Lallai dukkan kyakkyawan yabo da godiya na Allah ne. Muna gode MaSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa. Muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, kuma wanda Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abun bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai yake, ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa.
Ya ku ‘yan uwa masu daraja, yau kuma In Allah yaso zan dan yi bayani ne takaitacce kwarai game da ibadar layyah da muke fuskanta, kasancewar na ga ‘yan uwa da yawa sun bukaci yin hakan, domin ya zama tunatarwa da fadakarwa zuwa gare mu akan wannan ibadah mai muhimmanci.
Ina ganin ba sai na dauko dogon bayani da tarihi game da layyah ba, kasancewar da yawan mu ina ganin da ikon Allah sun san tarihin faruwar ibadar layyah, tun daga Annabi Ibrahim da dan sa Annabi Isma’il (AS), har zuwa lokacin Manzon tsira dan Abdullahi, Annabi Muhammad (SAW).
Don haka kawai zan dan yi bayani ne game da muhimman abubuwan da ya kamata mu sani game da wannan babbar ibadah, muhimmiya, ta layyah.
Ya ku jama’ah, a takaice, layyah ita ce abun da ake yankawa na daga dabbobin ni’ima (wato Bahimatul An’am), kamar rakuma, shanu, awaki da tumaki, a ranar yanka (wato ranar babbar Sallah) da kuma ranakun shanyar nama ko busar da shi (wato ayyamut-tashriq), da niyyar yin ibadar layyah. Sannan a bisa zance mafi inganci daga cikin zantukan Malamai shine, layyah Sunna ce mai karfi ga mai ikon yi (amma wasu malamai suna ganin idan mutum yana da halin yin layyah, to wajibi ce a gare shi).
Kuma lokacin yanka dabbar layyah shine, daga bayan Sallar idi na ranar babbar Sallah har zuwa karshen ranakun busar da nama (wato ranakun 10, 11, 12 da 13 kenan).
Sannan an sunnanta raba naman layyah kashi uku, wato mutum yaci kashi daya da iyalansa, yayi sadaka da kashi daya, kuma yayi kyauta da kashi daya.
Ya ku jama’ah, ku sani, layyah tana da falala mai girman gaske, domin abunda ke cikin ta na lada mai tarin yawa da kuma amfanar da talakawa, da kuma toshe masu hanyar roko domin bukatun su.
Sannan mu sani, ba’a yin layyah ko hadaya da komai sai abinda ya kasance na rakumi matashi mai akalla shekara biyar. Sannan da shanu ko maraki akalla mai shekara biyu. Sannan rago akalla mai watanin shida. Sai taure akalla mai shekara daya.
Sannan game da akuya da rago da taure da tunkiya, ko wannen su yana halatta ne ga mutum daya. Rakumi kuma ga mutane bakwai, sa ko saniya kuma su ma ga mutane bakwai. Kuma ya halatta mutum yayi layyah da akuya ko rakuma ko sa, ga kansa da kuma iyalansa. Kuma ya zama wajibi abunda za’a yi layyah da shi ya kasance mai lafiya, mara aibu ko wata matsala.
Kamar yadda kuka sani, yau muna ranar talata, 15 ga watan Dhul-Qa’dah, 1441 AH, wanda yazo daidai da 07/07/2020, kenan daga yau bai wuce saura kwanaki 25 mu shiga babbar Sallah ba, idan Allah yasa muna cikin masu yawancin rai, sannan ga shi kuma har yanzu cikin ikon Allah da kaddarawar sa, har yanzu muna cikin matsalar wannan annoba ta cutar korona. Don haka ina mai kira ga ‘yan uwana masu girma, masu daraja, da cewa don Allah mu zamanto masu bin umurnin likitoci da masana, da yin da’a da biyayya ga shugabannin mu akan wannan al’amari. Duk wata ka’idah da doka da aka shata muna, don Allah mu kiyaye. Muyi ta bin ka’idodi da dokoki, tare da dage wa akan rokon Allah da addu’a, Allah ya kare mu, kuma ya yaye muna wannan annoba. Sam bai kamata Musulmi ya zama mai taurin kai ba. Har kullun, ya kamata Musulmi ya nuna hali da dabi’un Musulunci a duk inda yake, ko a cikin ko wane yanayi ya samu kan sa.
Ina rokon Allah ya babu ikon ganin babbar Sallah lafiya, ya bamu hali da ikon sayen dabbar layyah, kuma ya bamu lafiya da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, a kasar mu Najeriya da kuma yankin mu na arewa baki daya. Kuma ina rokon Allah ya kare mu daga wannan cuta ta annobar korona, kuma ya nuna muna wucewar ta lafiya, amin.
Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawarka a koda yaushe.
Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah, Muhammad (SAW).
Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi a cikin dukkanin al’amurran mu, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761