Soke Hajjin Bana: An Fara Mayarwa Maniyyata Kuɗin su a Kano.

0
332

Daga Jabiru Hassan, Kano
Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta ce ta fara aiwatar da mayar da kuɗaɗen ajjiya da maniyyata suka biya domin tafiya Aikin Hajjin wannan shekara ta 2020, inda tuni ana ci gaba da maida kuɗaɗen ga maniyyatan da suka bukaci a basu haƙƙunan su.
Hajjreporters Hausa ta  sami jin ta bakin jami’ar yaɗa labarai ta hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi, inda ta sanar da cewa aikin maida kuɗaɗen yana tafiya cikin nasara.
Ta ƙara da cewa kwamitin da aka kafa domin rarrabba kuɗaɗen ga masu su ya dage wajen bin ƙa’idojin da suka wajaba wajen ganin an maidawa kowa haƙƙin sa ba tare da tsaiko ba.
Hajiya Hadiza ta ce” Babu shakka yanzu haka ana ci gaba da maida kuɗaɗen ga maniyyatan da suka bukaci a basu nasu, kuma Alhamdulillahi aikin yana tafiya cikin nasara da tsari duba da yadda babban sakataren hukumar ta jin dadin alhazai ta jihar kano  yayi kokari wajen tsara yadda shirin maida kuɗaɗen zai gamsar da kowane bangare Wanda hakan abin jin daɗi ne,” Inji ta.
Sai dai jami’ar Hulda da jama’ar ta bayyana cewa bisa ga yadda suke gani wajen maida kuɗaɗe ga maniyyatan, mafiya yawan su ba zasu karbi kuɗaɗen nasu ba duba da yadda alkaluman wadanda suka bukaci a maida masu da kuɗaɗen su ya nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here