Liman Aƙibu Ya Buƙaci Maniyyata Su Ƙara Haƙuri Kan Soke Hajjin Bana

0
7

Sheikh Aƙibu 
Daga Jabiru A Hassan, Kano
Limamin masallacin Juma’a na Ikwanil  Mustapha da ke Ɗan Rimi, Rijiyar Lemo a Jihar Kano, Sheikh Aƙibu  Sa’id Almuhammadi ya buƙaci maniyyata da suka biya kuɗaɗen tafiya aikin Hajjin wannan shekara da su ƙara haƙuri tare da addu’oi domin samun cikakkiyar waraka daga annobar Coronavirus wacce ta zamo barazana ga gudanar da wannan ibada.
Yayi wanna kiran ne a huɗubar da ya yi ranar Juma’a, tare da bayyana cewa soke aikin Hajjin bana  da hukumomin Saudiyya  su ka yi ya biyo bayan ƙoƙarin daƙile annobar Covid-19 ne,  wacce masana harkar kiwon lafiya su ka tabbatar da cewa akwai bukatar a rage cunkoson al’uma a dukkanin guraren ibada da kasuwanci da sauran guraren da al’uma ke taruwa.
Sheik Aƙibu ya kuma tunasar da cewa dakatar da zuwa aikin Hajji ba sabon abu bane, domin ko a zamanin Manzon Allah (SAW) an riƙa hana zuwa aikin Hajjin saboda wasu dalilai wanda kuma hakan yakan zamo tarihi wasu lokutan.
Ya kuma yabawa hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa watau NAHCON da kuma hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohi saboda ƙoƙarin da suke yi na mayar da kuɗaɗen da maniyyata suka ajjiye domin tafiya ƙasa mai tsarki cikin nasara.
Daga ƙarshe, limamin yayi fatan cewa wannan annoba ta Covid-19 zata zamo tarihi batare da jinkiri ba, sannan yayi addu’a ta ci gaba da samun dawwamammen zaman lafiya a duniya baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here