Hajjin 2020: Nassarawa ta fara karbar takardun neman maidowa alhazai kuɗaɗen su

0
8
Tun ranar 26 ga watan Yuni Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta fara karbar takardun neman maidowa da Maniyyata da suka bada kuɗaɗen ajiya haƙƙunan su a Jihar Nassarawa a ƙarƙashin Mallam Idris Ahmad Almakura.
Hakan ya faru ne sakamakon soke hajjin bana ga ƙasashen waje da Saudi Arebiya ta yi sakamakon annobar COVID-19.
Amma kuma duk waɗanda suke son su ci gaba da ajiye kuɗaɗen su domin Hajjin 2021 za su iya bari domin su za a fara kulawa da su a baɗin, yayin da waɗanda suke son karbar kuɗaɗen su za su iya yin hakan kafin ko ranar Juma’a, 24 ga Yuli.
Ana kira ga dukkan jami’an alhazai na jihar da su miƙa takardun neman maido da kuɗaɗen kafin ranar da a ka tsayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here