Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano ta yabawa IHR

0
475

 

Daga Jabiru Hassan, Kano

 

Sakataren Hukumar  Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Ɗambatta ya jinjinawa Ƙungiyar masu bada rahoton Aikin Hajji da Umara, da a ka fi sani da ta Independent Hajj Reporters saboda ƙoƙarin da take yi wajen bayyana haƙiƙanin abubuwan dake faruwa dangane da Aikin Hajji da Umara a kasar nan da kuma duniya baki ɗaya.

 

Yayi wannan yabon ne a tattaunawar su da wakilin mu yayin da hukumar ta ƙaddamar da maidowa maniyyatan da suka bukaci a mayar masu da kuɗaɗen su da suka ajjiye domin tafiya Aikin Hajjin bana wanda a ka soke.

 

 Ya kuma bayyana cewa wannan ƙungiya ta IHR ta cancanci a yaba mata duba da irin kokarin da take yi batare da nuna kasala ba.

 

Ɗambatta yace” babu shakka, IHR tayi fice wajen bayyana gaskiyar abubuwan dake wakana walau a hukumomin kula da jin daɗin alhazai  a faɗin ƙasa da yadda take bada rahotanni na abubuwan da suke faruwa a faɗin duniya ta yadda al’uma za su ƙara samun ilimi kan dukkanin wasu rukunai na gudanar da Hajji da Umara cikin nasara”. Inji shi.

 

Bugu da ƙari, Shugaban hukumar ya sanar da cewa hukumar tana samun kyawawan nasarori wajen mayar wa da maniyyata kuɗaɗen su batare da samun wata matsala ba.

 

 Sannan ya yi bayani cewa a cikin alhazai fiye da 1,700, maniyyata fiye da 300 ne kawai suka buhaci a mayar masu da kuɗaɗen su ya zuwa wannan lokaci, in da ya ce hakan ya nunar da cewa maniyyatan da suka bar kuɗaɗen su sun ninka waɗanda suka bukaci a mayar masu dash a jihar Kano.

 

Ɗamambatta yayi amfani da wannan dama wajen yin godiya ta musamman ga gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda yadda ya ke baiwa hukumar tasa dukkanin kulawar da take da buƙata.

 

 Sannan ya yaba da kwazon ma’aikatan hukumar manyan su da ƙanana wanda hakan ta sanya ake ci gaba da samun kowace irin nasara a hukumar kamar yadda take gani a yau.

 

Hajjreporters Hausa ta sami zantawa da wasu  maniyyata da suka karbi kuɗaɗen su watau Malam Aminu Sabo daga karamar hukumar Tarauni da kuma malama Nana Fatsuma Usman waɗanda suka bayyana cewa ko shakka babu, hukumar ta ciri tuta wajen kyautata wa maniyyata da kuma yi masu dukkanin abubuwan da suka kamata batare da gajiyawa ba.

 

San nan ya yi alkawarin cewa zasu ci gaba da addu’oi domin ganin annobar Covid-19 ta zamo tarihi a duniya baki ɗaya.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here