Mataimakin Kwamandan Jami’an Tsaro na musamman a Masallacin Harami a lokacin Hajji, Manjo Janar Mohammed Bin Wasl Al-Ahmadi ya bayyana cewa za a ci gaba da rufe babban masallacin mai tsarki har a ranar Arafa da Eid Al-Adha, wato Babbar Sallah, a wani mataki na daƙile ci gaba da yaɗuwar annobar coronavirus.
“Dakatar da sallah da a ka yi a ciki da wajen babban masallacin harami na Makkah na nan daram. Saboda haka nu na kira ga al’umma da su yi buɗe baki na azumin arfa a gudajen su,”
Manjo Janar Al-Ahmadi ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai ranar Talata, inda ya kuma bayyana cewa an kammala kashin farko na tsare-tsaren Aikin Hajjin bana.
Ya kuma ce tsarin tsaro na bana zai maida hankali ne a kan shirye-shirye, tsaro, kula da ɗan’adam da kuma lafiya.
“Za mu maida hankali a kan lafiya saboda wani yanayi na daban da muka tsinci kan mu. Nan da kwanaki kaɗan za mu ƙaddamar da ragowar tsare-tsaren,” in ji Al-Ahmadi.
Ya kuma ƙara da cewa an kawo wani sabon tsari na lura da shige da fice a babban masallacin domin a tabbatar da bada tazara.
A wani mataki na kariya kuma, an fitar da hanyoyin shiga gurin yin ɗawafi da Sa’ayi, wato safa da marwa, inda ya ƙara bayyana cewa waɗanda suke da suke da goron gayyata a hukumance, za a ba su damar shiga harabar masallacin.
|
|
Ba za a buɗe Masallacin Harami ran Arfa da ran Sallah ba
|
|