Ministan Hajji da Umara na Saudi Arebiya, Dakta Mihammed Saleh Benten, a yayin da yake ziyarar duba aikace-aikace da tsare-tsare na Hajjin bana ya bayyana cewa shirin na bana ba a taba yin irin sa ba inda zai sauƙaƙawa alhazai su yi ibadar cikin sauƙi da nutsuwa.
“Hukumomin tsaro, lafiya da aikace-aikace ne za su aiwatar da wannan gagarumin shirin da a ka tanada. Tsare-tsaren sun haɗa da samar da kiwon lafiya da ba a taba samun irin sa ba da kuma tsarin lura da cunkoso gangariya da za a auwatar da shi a kan ƙadamin bin ƙa’idojin kariya daga yaɗuwar cututtuka wanda Hukumar lafiya ce ta samar da shi domin kare alhazai daga kamuwa da annoba,” in ji shi.
Benten ya kuma jinjinawa ƙoƙarin da Hadimin Masallatai biyu masu tsarki, Sarki Salman da ɗan sa Yarima Mohammed Bin Salman wajen aiwatar da Aikin Hajjin bana ta duba da matakan kariya domin tsare alhazai daga kamuwa da dukkan nau’in cututtuka.
Kafin nan, Ministan ya rangadin duba tsaren-tsaren tarba da makwancin alhazai a wani otal mai suna Four Point Hotel a Makka. Kana ma’aikatan hukumar sun bashi bayanai a kan tasrin da a ka yi na tarba da makwancin alhazai da za su zauna daga 4 zuwa 8 ga Dul Hijja kafin su bar Mina.
Sannan Benten ya ziyarci tantunan alhazai a Arafat da kuma kayan aikin da ke Muzdalifah. Daga bisani ya cigaba da ziyarar duba aiki zuwa birnin tantuna na Mina inda bai tsaya ba sai a wani dogon gini da a ka tanadeshi domin alhazai, inda ya nuna gamsuwa da irin tsari da kayan aikin da a ka tanada, musamman bangaren makwanci da abinci ga alhazai.
A ƙarshen ziyarar, Minustan ya kalli majigi na tsare-tsaren aikace-aikace da a ka tanada domin alhazai lokacin tafiyar da za su yi daga makwantan su zuwa Jamrat domin yin jifa