HR ta yabawa Kano kan mayar da kuɗaɗen maniyyata

0
439
I

Daga Jabiru Hassan, Kano
Kungiyar Ƴan Jaridu Masu Bada Rahotannin Aikin Hajji da Umara (IHR) ta nuna gamsuwar ta bisa yadda Hukumar Kula da Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano ta gudanar da aikin mayarwa da  maniyyata kuɗaɗen su cikin nasara.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kodinetan kungiyar na ƙasa,  Malam Ibrahim Mohammed, IHR ta jinjinawa hukumar alhazai ta jihar bisa yadda shirin mayar da kuɗaɗen ga maniyyata ya kasance cikin yanayi mai gamsarwa da kuma tsari, wanda kuma hakan ya ja hankalin ƙungiyar ta yaba mata.
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa yadda hukumar ta gudanar da mayar da kuɗaɗen ya nuna cewa shugaban hukumar,  Alhaji Mohammed Abba Dambatta da ɗaukacin  ma’aikatan sa sun cancanci yabo da fatan alheri, musamman ganin yadda suka sanya kowane bangare cikin sha’anin mayar da kuɗaɗen ga maniyyata kamar yadda aka shaida.
 Daga nan sai IHR ta buƙaci dukkanin sauran hukumomin kula da Aikin Hajji na jihohi suyi koyi da hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano domin tabbatar da cewa komai yana tafiya cikin nasara, tareda fatan alheri ga hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here