RAHOTO NA NUSAMMAN: Sanya ido da Hajj Reporters ke yi kan maidowa maniyyata kuɗaɗen su yana tasiri

0
391

Daga Jabiru Hassan, da Mustapha Adamu, Kano

 

Babu shakka kiran da Ƙungiyar Ƴan Jaridu Masu bada Rahotannin Hajji da Umara, wacce a ka fi sani da Independent Hajj Reporters (IHR) yana tasiri a hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohi.

 

A tuna cewa Saudi Arebiya ta soke Hajjin 2020 ga ƙasashen waje. Ƙasar ta yanke cewa iya mazauna ƙasar ne, kuma mutuma 10,000 ne za su yi Aikin Hajjin na bana, lamarin da ya sanya ƙasashe suka ɗauki matakin mayarwa maniyyata kuɗaɗen su da suka biya, ciki har da Nijeriya.

 

Domin tabbatar da an maidawa maniyyatan da suka nemi a maido musu da kuɗaɗen haƙƙunan na su cikin gaskiya da amana, IHR ta fitar da sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kodinetan ta na ƙasa, Mallam Ibrahim Muhammad , ta ja kunnen Hukumomin Kula da Jin daɗin Alhazai na Jihohi da su tabbatar sun maidawa kowa kuɗin sa ba tare da almundahana ba. 

 

Ta kuma yi kira ga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta tabbatar hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi sun baiwa duk wanda ya nemi a bashi kuɗaɗen sa ya samu, inda itama ƙungiyar ta ci alwashin za ta sanya ido domin tabbatar da aikin maida kuɗaɗen ya samu nasara.

 

Haka kuwa a ka yi, domin haƙiƙa wannan mataki da ƙungiyar ta ɗauka ya sanya ake cimma kyawawan nasarori wajen ganin maida kuɗaɗen ga maniyyatan da suka buƙaci a basu nasu.

 

Wani bincike da wakilan mu suka gudanar ya nuna cewa ko shakka babu IHR tana taka muhimmiyar rawa wajen ganin ana gudanar da Aikin Hajji da Umara a wannan ƙasa cikin cikakkiyar nasara, duba da yadda a kowace shekara ake samun wasu sauye-sauye daga hukumomin ƙasar Saudiyya, kamar yadda ake gani cikin shekaru masu yawa.

 

Dukkanin jami’an dake aiki a hukumomin kula da jin daɗin alhazai da Hajj Reporters Hausa ta zanta da su daga Jihohin Kano, Jigawa da Katsina sun  bayyana cewa yadda IHR take bibiyar aiyukan hukumomin yana taimakawa wajen aiwatar da aiyuka da suka shafi maniyyata tun daga gida zuwa ƙasa mai tsarki batare da nuna kasala ba.

 

Haka kuma IHR ta kasance mai matuƙar muhimmanci ga su kansu hukumomin kula da jin dadin alhazai dake jihohi tare da ƙara musu ƙarfin gwiwa wajen yayata aikace-aikacen da suka yi waɗanda suka shafi aikin Hajji da Umara, musamman ganin cewa ƙungiyar ta kasance abar misali ta fannin isar da saƙonni da suka shafi aikin Hajji da Umara.

 

A ƙarshe, binciken ya nuna cewa akwai bukatar ganin cewa IHR ta faɗaɗa aiyukan ta zuwa kamfanonin shirya tafiye-tafiye watau Travelling Agencies, da hukumomin kula da filayen jiragen sama wato FAAN da kamfanonin jiragen sama ta yadda kowane bangare zai amfana daga ƙungiyar

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here