Hajjin 2020: A maidowa da maniyyata kuɗaɗen su ta banki – Sugaban NAHCON

0
366

 

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Barista Zikrulla Kunle Hassan ya yi kira ga Hukumomin jin Daɗin Alhazai na Jihohi da su biya waɗan da suka nemi a dawo musu da kuɗaɗen su ta asusun banki.

 

A tuna cewa sakamakon bullar annobar COVID-19, Saudi Arebiya ta yanke hukuncin yin Aikin Hajjin bana amma ga mazauna ƙasar kawai.

 

Wannan matakin ne ya sanya hukumomin aikin Hajji na duniya su ka fara maidawa maniyyata kuɗaɗen su da suka riga suka biya, ciki har da Najeriya.

 

Yayin ganawa da manema labarai ranar Alhamis, Bar. Hassan ya shawarci maniyyatan da su ka nemi a dawo musu da kudaɗen su da su buɗe asusun banki saboda ta nan za a biya su haƙƙunan nasu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here