Hajjin 2020: Lafiyar alhazai ita muka sa a gaba- Saudiya

0
219

 

Shirye-shiryen aikin Hajjin bana zai fi maida hankali ne a kan ɗaukar ƙwararan matakan kare lafiya, in ji wani Jami’in aikin Hajji, Alaa Al-Nofaie.

 

“Aikace-aikace da kuma bibiya shine abin da ake ta yi a kullum domin tabbatar da cewa ayyukan da ake yi a masallacin harami mai tsarki na Maka an shirya shi tsaf duk da cewa alhazan na bana basu da yawa”.

 

Sama da ma’aikata 3,500 ne su ke aikin tsaftace babban masallacin Haramin na Maka, inda Ofishin Babban Jami’in Kula da Masallaatai biyu Masu Tsarki ne ke kura da ayyukan tsaftacewa da feshin magungunan.

 

Haka kuma ma’aikatan suna amfani da lita 54 na sinadaran feshin ds ba ya cutarwa sannan akwai injina 95 da ake amfani da su a aikin.

 

Gwamnan Makka, Mohammed Abdullah Al- Quwaihis ya bayyana cewa duk da yaɗuwar annobar COVID-19 a ƙasar bai kai na nahiyar turai ba, wajibi ne ƙasar ta ɗauki dukkan matakai na kariya a kan cutar.

 

Ya kuma bayyana cewa duk da irin naƙasun da ƙasar ta samu a kan tattalin arziki sakamakon soke Umara, Saudiya ta ɗauki ƙwararan matakai na kare musulmai.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here