Daga Mustapha Adamu
Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ƙaryata wani rahoto da jaridar The Guardian ta buga a ɗab’in ta ranar 24 ga watan Yuli, cewa kuɗaɗe kimanin Naira biliyan 150 na alhazan Nijeriya sun maƙale a Saudi Arebiya sakamakon soke aikin Hajjin bana ga ƙasashen waje.
Rahoton ya nuna cewa waɗan nan kuɗaɗen na hidimomin alhazan Nijeriya ne da a ka biya kamfanoni a Saudiya domin Hajjin bana.
Waɗan nan kudaɗen da a ke zargin sun maƙale sun haɗa da waɗanda a ka biya kamfanonin sufurin jiragen sama, sufurin motoci, masu harkar Hajji, Hukumomin kula da jin daɗin alhazai da sauran su.
Amma kuma marubucin ya faɗi adadin kudaɗen ba tare da bayyana wanda ya biya kuɗaɗen ba, in ji sanarwa mai wacce Jami’ar yaɗa labarai, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu ranar Juma’a.
Sanarwar t ce ya kamata a sani cewa a ranar 22 ga watan Yuni Saudiyya ta yanke shawarar soke aikin Hajjin bana, kuma kafin nan ta dakatar da aikin Umara ranar 27 ga Febrairun 2020, sannan ta bada umarnin a dakatar da duk wani shirin aikin Hajjin bana a ranar 31 ga watan Maris.
Sannan Saudiya ta yi gargaɗi a kan cigaba da duk wata hada-hadar kuɗaɗe ko kuma ajiya har sai ta bayar da izni, sabo da haka a wanne lokaci ne aka biya waɗan nan kuɗaɗen?
Ta ƙara da cewa tun da Saudiya ta sanya wannan sharaɗin, NAHCON ba ta ƙara ba da lasisi ba ga wata Hukumar jin Daɗin Alhazai ko kamfanonin sufuri masu zaman kan su domin tana jiran izini ne daga Saudiya.
Sanarwar ta yi bayanin cewa kawai dai NAHCON ta karbi takardun neman yin jigilar aikin Hajjin sannan ta tantance masu neman, kana ta ajiye bayanan su har sai ta ga matakin da Saudiya ta ɗauka. Sabo da haka har yanzu babu wanda a ka bawa lasisin aikin Hajjin 2020.
“Ya kamata a tuna cewa Shugaban NAHCON, Barr. Zikrulla Kunle Hassan ya sha faɗin cewa har yanzu NAHCON bata biya kowa a kan aikin Hajji ba ko a Saudiya ko a nan gida Nijeriya domin Hanjin 2020.
” Kuma ya kamata a sani cewa a lokacin da sababbin Jami’an hukumar suka fara aikin samar da makwanci da abinci a ƙasa mai tsarki batun dakatar da Hajji ya taso a ƙasar kuma tun daga nan baa sake yin wani shiri a kan aikin Hajji ba.
“Tabbas NAHCON ta bada umarnin karbar kudaɗen ajiya ga hukomomin jin daɗin alhazai na jihohi, amma kuma ta yi hakan ne da shirin ko da ba samu damar yin Hajjin bana ba, to nan take za a fara maidawa maniyyata kuɗaɗen su,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa tuni Hukumomin jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kamfanunuwan harkar Hajji da Umara ma su zaman kan su suka fara maidawa maniyyatan da suka biya kuɗaɗen su.
A ƙarshe Usara ta ja hankalin kafafen yaɗa labarai da su riƙa rubuta labaran gaskiya ba shaci faɗi ba.
Ta ƙara da cewa a shirye NAHCON take da ta rima taimakawa duk wani mai nrman bayanai a gurin ta da bayanan da suka dace, amma abin takaici ne a riƙa bata ƙwarewar aiki sabo da son zuciya.