Hukumar Lafiya ta Saudi Arebiya ta ƙara ƙarfafa kiwon lafiya ga mahajjata a yayin da suke ibada, inda ta samar da ɗakin magani a kowanne gidan da alhazai suka sauka sannan kowanne ayari na mahajjata ɗin za a haɗa shi da wani gungu na likitoci domin kiwon lafiyar su.
Za a haɗa alhazan da gungun likitoci da bada kulawar gaggawa inda haɗa su da kayan aiki a kowanne lungu da saƙo domin yiwa baƙin Alkah hidima.
Hukumar ta samar da wajajen kiwon lafiya a gurare masu tsarki da bada kulawar lafiya ta musamman a asibitin Al-Wadi da kuma cibiyoyin kiwon lafiya 29 a Arafat, asibitocin da kuma asibitocin sha ka tafi da a ka tanade su don kiwon lafiya mai zurfi gami da motocin kiwon lafiya masu kayan aikj na gani na faɗa guda 6.
Gwamnatin ƙasar ta tanadi duk wannan tanadin kiwon lafiyar ne domin kariya da kulawa da baƙin Allah a yayin aikin Hajji